Wani Shaida Ya Ce Ya Biya kuɗin Fansa Miliyan N80 Ga Tukur Mamu Domin Fansar Mahaifiyarsa da Kanwarsa
Wani shaida da ake kira PW-D (Aka boye sunansa) ya bayyana a kotun tarayya da ke Abuja inda ya shaida wa Alkali ya biya fansar Naira miliyan tamanin domin kubutar da mahaifiyarsa da ‘yar uwarsa ga fitacen dan jaridar nan Tukur Mamu bayan hari da aka kai kan jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a shekarar ta 2022.
Read also: Wani Sanata A Nijeriya Ya ce Sun San Manyan Hafsoshin Sojan Da Suke Hakar Ma’adanai Babu Izini
Da yake magana a gaban mai shari’a Inyang Ekwo a ci gaba da shari’ar Tukur Mamu, wanda ake zargi da shiga tsakanin masu garkuwa da mutane tare da karbar makudan Kuɗaɗe domin kaiwa ‘yan ta’adda, Mamu yana fuskantar tuhume-tuhumen ta’addanci, mutumin ya ce an sako ‘yan uwansa tare da wasu mutane biyu.
Da yake tambaya ga mai bada shedar, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Lauya David Kaswe, PW-D ya sanar wa da kotu ya ce a ranar 28 ga Maris, 2022, ya samu labarin cewa mahaifiyarsa da ‘yar uwarsa suna cikin jirgin da aka kai harin, inda aka yi garkuwa da wasu fasinjoji, aka kuma kashe wasu. Washegari ya neme su a wani asibitin Kaduna amma bai ga alamun su ba. Mako biyu bayan harin, ya sami kiran waya daga masu garkuwan, waɗanda suka bar shi yayi magana da ‘yar uwarsa.
Ka Iya Karanta Wanna:Wani Sanata A Nijeriya Ya ce Sun San Manyan Hafsoshin Sojan Da Suke Hakar Ma’adanai Babu Izini
A cikin makonni biyu na gaba, ya ci gaba da tattaunawa da masu garkuwan, waɗanda a farko suka bukaci ya biya Naira miliyan 200 ga kowanan su a matsayin kuɗin fansa. Yayin da tattaunawar ke ci gaba, an ba shi sunayen ‘yan jarida huɗu ta hanyar da za a iya gudanar da tattaunawar. Duk da yake uku sun ƙi, kawai Tukur Mamu ya yarda ya zama mai shiga tsakani.
Read also: An Caka wa Malamin Addini Wuka a Sakkwato, Masu Ibada Sun Kashe Wanda Ake Zargi
PW-D ya shaida cewa ya sanar da jami’an gwamnati, ciki har da tsohon Babban Hafsan Tsaro Gen. Lucky Irabor da tsohon Darakta Janar na DSS Yusuf Bichi, game da mu’amalarsa da Tukur Mamu. Bayan wani lokaci, masu garkuwa da mutanen sun daina sadarwa kai tsaye da shi, suna magana kawai ta hannun Mamu.
Bayan tattaunawa mai tsawo, adadin kuɗin fansar ya ragu daga Naira miliyan 200 zuwa Naira miliyan 80. A watan Agusta 2022, PW-D ya bayar da kuɗin ga Mamu a Kaduna, wanda ya canza shi zuwa dalar Amurka. Mako biyu daga baya, Tukur Mamu ya nemi karin kuɗi don su zumanto $120,000.
Shaidan ya tabbatarwa da kotun yadda ya bi umarnin Mamu kuma ya kai kuɗin fansa tare da wasu kayayyakin da suka bukata, inda daga bisani suka sami ‘yanci wato suka sako mahaifiyarsa da kuma kanwarsa da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su.
Da yake amsa tambayoyi Babban lauya, shaidar ya tabbatar da cewa ba shi da wata hanyar sadarwa ta kai tsaye tsakanin Babban Hafsan Tsaron kasa da Mamu ba. Har ila yau, ya ce ya lura wani tsohon kwamishina ne ya yi shawarwari da Mamu a madadinsa.
Read also: Sarakunan Jama’are Da Ningi Na Miƙa Ta’aziya Bisa Rasuwar Durbin Kano
Ka Iya Karanta Wanna:DABARUN KIWON KAJI A LOKACIN YANAYIN SANYI (1)
Gwamnatin tarayya tana zargi Tukur Mamu da taimaka wa ayyukan ta’addanci ta hanyar karbar makudan Kuɗaɗe daga iyalan waɗanda aka sace a madadin kungiyar Boko Haram. Masu gabatar da ƙara sun yi ikirarin cewa ya yi amfani da dala 420,000 da kuma Naira miliyan 21 na kuɗin fansa da kuma boye kudaden haram a gidansa da ke Kaduna. A inda Tukur Mamu ya musanta dukkan tuhumar da ake masa. (NAN)




























