Connect with us

Hi, what are you looking for?

Uncategorized

Sarakunan Jama’are Da Ningi Na Miƙa Ta’aziya Bisa Rasuwar Durbin Kano

Sallar Jana'iza
Sallar Jana'iza

Masu Martaba Sarkin Jama’are da Ningi Na Miƙa Ta’aziya Bisa Rasuwar Durbin Kano

Daga Sunusi K/Naisa

Mai Martaba Sarkin Jama’are , Mallam Nuhu Ahmad Wabi, da Mai Martaba Sarkin Ningi, Alhaji Haruna Yunusa Muhammad na miƙa ta’aziyya bisa rasuwar Maigirma Durbin Kano, Alhaji Dr Muhammad Hassan Lawan Koguna.
Marigayi Durbi babban amini ne ga marigayi Sarkin Jama’are Ahmadu da marigayi Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Muhammad Danyaya. Hamshakin Dan Kasuwa Kuma Fitaccen Masanin Harkar Inshora.
Alhaji Hassan Koguna ya rasu a juya Jumma’a yana da shekaru 87 a duniya. Shine Shugaban Kamfanin Inshora Mai Tsohon Tarihi ta Koguna Ba6ura Insurance. Ya rike Mukamai da dama ciki har da shugabancin Kamfanonin Inshora ta ƙasa, da Kungiyar Wasan golf ta Kano Kuma ya kasance ƙaramin Jakadan a ƙasar Turkiya Mai kula da Jihohin Arewa guda 19.
Marigayi Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Abdullahi Bayero shi ya fara naɗa Alhaji Hassan Koguna sarautar Makaman Gado da Masun Kano, daga bisani kuma ya ɗaga darajar sarautar zuwa Durbin Kano Babbar sarautar da Dan Uwansa marigayi Alhaji Abdulkadir Koguna ya rike har zuwa rasuwarsa a 1971. Allah Yaji kansa, tare da dukkan magabatanmu .

Ga Wani Labarin:Ko Me Yasa Tsoho Ɗan Shekara 100 Har Yanzu Bai Sare Da Neman Halali Ba?

Da misalin karfe 10:00 Na safiyar yau Asabar ne, 10 ga Watan Jummada Ula 1447AH ( 1November 2025), aka sallaci marigayi Durbin Kano bisa jagorancin babban Limamin Masallacin Jumma Farfesa Muhammad Sani Zahardeen haka kuma Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da Mai Martaba Sarkin Jama’are, Mallam Nuhu Ahmad Wabi da manyan mutane da dubban jama’a na daga cikin waɗanda suka samu halartar saallar jana’iza ta marigayi Durbin Kano, Dr Muhammad Hassan Lawan Koguna a fadar Kano.

Ga Wani Labarin:Magidanci Mai Mata 2 Ya Kashe Ɗan Achaɓa Don Samun Kuɗin Ƙarin Aure

Durbin Kano ya rasu ya bar iyali da ‘ya’ya da jikoki. Jaridar TSN tana mika ta’aziya ga iyalai da ‘yen uwa da fadar Kano da Gwamnatin Kano gami da Shugaban mu Alhaji Bello Sani Galadanchi bisa wannan babban rashe da jihar Kano da ƙasa baki ɗaya. Allah Ya gafartawa Durbin Kano.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...