Ko Me Yasa Tsoho Ɗan Shekara 100 Har Yanzu Bai Sare Da Neman Halali Ba?
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Dangote Ya Sanya Wa Hanya Suna Tinubu, Zai Kashe N900 Biliyan Don Gina Hanyoyi A Najeriya
Wani dattijo me shekara 100 da haihu Alhaji Ibrahim Danjuma Mai Tsintsiya dake jihar Bauchi, ya ce har yanzu duk da shekaru da suka cimmasa bai fasa yawan talan sayar da tsintsiya ba, ba don komai ba sai don ya rufawa kansa da iyalansa asiri.
Dattijo Danjuma mai tsintsiya ya bayyana wa wakilinmu haka da ya ke zantawa da shi a cikin garin Bauchi.
Ya ce duk da halin da ake ciki da samari ke fama da rashin aikin yi da mutuwar zuciya shi har yanzu yana ci gaba da sana’ar sa ta sayar da tsintsiya wacce ya shafe shekaru 60 yana gudanarwa.
Dattijon ya ce ” A wuni ina sayar da tsintsiya daga ɗaya zuwa goma kuma da haka na ke ciyar da bakina da matana guda biyu da yarana goma da na haifa, duk da a yanzu uku ne ke raye”. Ina ji Alh. Ibrahim.
Ga Wani Labarin:Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranar Ziyarartar Makarantun Kwana
Alh. Ibrahim Mai tsintsiya, ya jaddada cewa da sana’ar sayar da tsintsiya ya samu rufin asiri dai-dai gwargwado tare da ilimintar da ‘yayensa gami da basu tarbiyya gwargwadon iyawarsa.
Read also: Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta Ce Dole A Rage Farashin Burodi, ta Kafa Kwamitin Don Magance Matsalar
Yace tun ana sayen Mota roka naira dubu biyar yake kasuwanci, Kuma matarsa a yanzu ta kusa shekara 80 da haihuwa, amma har izuwa yanzu yana shiga sako da lungu domin talan tsintsiya kamar yadda ya saba, kuma Allah bai hanashi samun rabon sa ba.
Dattijon ya ce ya kamata matasa su zage damtse domin neman na kansu, don su rufawa kansu asiri. Inda ya ce lokacin yawan maula da banbaɗanci a Najeriya ya hucce domin kuwa bashi da wani alfanu a rayuwa.
Danjuma maitsintsiya ya ce a sanadiyar sana’arsa mutane kan tsai da shi su taimaka masa batare da ya nemi taimakon su.
A saboda haka ya ce ba zai manta da Sarkin Bauchi Mai martaba Rilwanu Sulaimanu Adamu ba, saboda ya taba sa an kira shi har fadarsa ya kuma yabamasa bisa ƙoƙarin neman halal da yake domin tsira da mutunci, ya kuma ɗauki kuɗi har naira dubu 20 ya ba shi domin ya ƙara jari.
Ya godewa Allah da ya bashi tsawon rai da kuma lafiya da har ya samu damar neman na halali tare da sauke nauyin iyalansa.
Wakilinmu yayi duba na tsanaki game da yabawa kokarin Ma’aikatar Jin dadin Jama’a da walwala ta jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Hajiya Hajara Yakubu Wanka, bisa ƙoƙarin ta wajen karrama mutane irin su Danjuma masu neman abin kansu da lambar yabo da kuma tallafa musu da jari don bunkasa sana’ar su.
A bisa wannan kyawawan ayyukan alheri na wannan Ma’aikata ke gudanarwa ya ke godon Kwamishina Hajara da idanunta yai duba ga Alhaji Ibrahim Danjuma mai tsintsiya duba da kankantar jarinsa da kuma yawan shekarunsa da har yanzu zuciyarsa bata karaya ba wajen neman halal, don ƙarfafa masa gwiwa.
Read also: IMAM ABDURRAHMAN DA UWARGIDAN GWAMNAN BAUCHI SUN TAIMAKI MATA KAN INGANTA SANA’AR ROGO
Ga Wani Labarin:“Na Fasa Auren Yar Guda”, In ji Mai Wushirya
Ibrahim Mai tsintsiya mazaunin ne a unguwar Jahun Gulmammu a cikin garin Bauchi, haka kuma yana zama a kusa da gidan man Total da ke wunti a Bauchi don ci gaba da kasa hajjarsa ta tsintsiya domin sayarwa ga jama’a.




























