IMAM ABDURRAHMAN DA UWARGIDAN GWAMNAN BAUCHI SUN TAIMAKI MATA KAN INGANTA SANA’AR ROGO
Daga Muazu Hardawa Bauchi
Babban Sakatare a hukumar jin dadin alhazai ta jihar Bauchi Dujuman Bauchi, Dr. Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, ya ƙaddamar da rabon tallafin kayan abinci da ake sarrafawa da rogo da kuɗi N15,000 ga mata 250, don agaza wa matan bunkasa Sana’ar abinci mafi araha ta wannan fannin. Tallafin wanda Uwar Gidan Gwamnan Jihar Bauchi Hajj Dr Aisha Bala Muhammad ta bayar ga wanda suka ci moriya, an rabawa mata domin tallafa musu da ƙarfafa musu guiwa wajen dogaro da kai da inganta rayuwarsu a fannin dogaro da kai.
Ranar Talata 18 ga watan Agusta 2026, Dujuman Bauchi, Dr. Imam Abdurrahman Ibrahim Idris, ya ƙaddamar da rabon tallafin kayan da kuma rogo da kuɗi N15,000 ga mata 250, a wani yunƙuri na tallafa wa matan.
Tallafin, wanda Uwar Gidan Gwamnan Jihar Bauchi ta bayar, an rabawa mata 250 domin rage musu raɗaɗin matsin tattalin arziki tare da taimaka musu wajen inganta rayuwarsu da ta iyalansu.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da rabon tallafin, Dujuman Bauchi Sheikh Abdurrahman Ibrahim Idris ya bayyana cewa irin wannan tallafi na da muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa wa mata, musamman ta hanyar samar musu da abin da za su dogara da shi wajen gudanar da ƙananan sana’o’i da sauran harkokin dogaro da kai.
Read also: IMF Ta Ce Bata Da Hannu A Janye Tallafin Man Fetur A Nijeriya
Aƙalla Ɗalibai Mata Dubu 12,133 Zasu Sami Tallafin Karatu Na AGILE A Bauchi
Read also: Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta Ce Dole A Rage Farashin Burodi, ta Kafa Kwamitin Don Magance Matsalar
Ya kuma yaba da wannan mataki na Uwar Gidan Gwamnan Jihar Bauchi, yana mai cewa tallafin zai taimaka wajen inganta rayuwar waɗanda suka amfana da shi tare da ƙarfafa musu gwiwa wajen neman abin dogaro da kansu.
Matan da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikinsu, tare da godiya ga Uwar Gidan Gwamnan Jihar Bauchi da Dujuman Bauchi bisa wannan tallafi da suka ce zai taimaka musu wajen fuskantar ƙalubalen rayuwa.
Read also: Ko Me Yasa Tsoho Ɗan Shekara 100 Har Yanzu Bai Sare Da Neman Halali Ba?
HISBAH A BAUCHI TA HUKUNTA MATASAN DA SUKA DAURA AUREN SADAKIN N3000
Wannan tallafi ya sake nuna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki wajen tallafa wa mata da ƙarfafa su domin su kasance masu dogaro da kansu da kuma taka rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin iyalansu da al’umma baki ɗaya.




























