Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Za a Fara Jigilar Alhazan Jihar Bauchi Daga Ranar 7 Ga Watan Mayu

Imam Abduraham
Imam Abduraham

Za a Fara Jigilar Alhazan Jihar Bauchi Daga Ranar 7 Ga Watan Mayu

Daga Muazu Hardawa Bauchi

Babban Sakataren Hukumar Jin dadin Alhazai Ta Jihar Bauchi Imam Dr. Abdurrahman Ibrahim Idris (Dujuman Bauchi) Ya Bayyana Cewa Hukumar Za ta Fara Jigilar Alhazanta Daga Ranar 7 ga watan Mayu, Yadda za a Dauke Su a cikin Jirage Shida 6. Kuma Za su Tashi Ne A Filin Jirgin Saman Kasa Da Kasa Na Sir Abubakar Tafawa Balewa Dake Bauchi.
Imam Abdurrahman Yace Ranar 4 Ga Watan Mayu Za’a Fara Tashi da Alhazan Jos Zuwa Ranar 7 Ga wata Sai Bauchi Su Fara Tashi Da Sauran Alhazan Bauchi.
Imam Abdurrahman Ya Bayyana Hakan Ne A Zaman Ganawa Da Kwamitin Yada Labarai Na Ayyukan Aikin Hajji da Jigilar Alhazai Zuwa Kasa Mai Tsarki Da kuma Dawo da su Bayan Kammala Aikin Hajji Na Shekarar 2026.
Shugaban Kwamitin Babban Sakataren Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi Alh Shehu Yahaya Jalam Ya ja Hankalin ‘Yan Jarida su Tsaya Wajan Bayyana Gaskiya da kuma Yin Hira Da Masu Ruwa Da Tsaki Kan Aikin Hajji Kan Abin da Ke Faruwa Akan Alhazai Da kuma Jigilar Su Zuwa Saudiya da Abin da ke Faruwa A Can.
Shehu Yahaya Jalam. Yace ‘Yan Jarida Su Ba da Hadin Kai Wajen Labarai Wanda Za Su Daukaka Jihar Bauchi.
Daractan Fadakarwa da Wayar da. Kai Malam Hashimu Abubakar Sadiq Ya Jinjina tare da Godiya Wa ‘Yan Jarida Domin Gagarumar Gudummowa da Suke Ba wa Hukumar A duk Lokacin Da Aka Neme Su Cikin Kankanin Lokaci Za su Zo, don haka Suna Godiya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...