Gwamnatin Kano ta Ce Dole A Rage Farashin Burodi, ta Kafa Kwamitin Don Magance Matsalar
Daga Rabi’u Sani
Read also: Gwamnatin Kano Ta Naɗa Sheikh Bazzallah Nasir Kabara A Matsayin Shugaban Hukumar Tace Fina-finai
A kokarinta na ganin an samu sauƙin matsalolin tattalin arzikin da ke addabar mazauna jihar, gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin mai girma Alhaji Abba Kabir Yusuf ta kafa kwamitin da zai magance da kuma daƙile tashin farashin burodi a fadin jihar.
Kwamishinan Zuba Jari, Kasuwanci, Masana’antu da Haɗin Gwiwa, Alhaji Gwani Shehu Wada Sagagi ne ya sanar da hakan, a yayin wani taro da masu ruwa-da-tsaki da ya gudana a ranar a dakin taro na ma’aikatar a ranar Asabar da ta gabata.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Sanar da Hutun Bikin Takutaha
Taron wanda ya kunshi manyan masu yin burodi, kungiyar ci gaban kasuwar Singa, da kuma kungiyar kare hakkin masu amfani da kayayyaki. Kwamishina Sagagi, ya ce an kira taron ne saboda tsananin damuwar da Gwamnan ya nuna game da halin kuncin da ‘yan jihar Kano ke fuskanta sakamakon tsadar burodi da kayan abinci na yau da kullun.
A Iya Karanta Wanna:Majalisar Matasan Arewa ta nuna damuwa da matsanancin rashin wutar lantarki a Kano
Bayan shawarwari masu inganci, an kafa wani kwamiti mai mutane bakwai tare da gudanar da waɗannan aiyyuka kamar haka:
-Daidaita Nauyi da Ma’auni Burodi: Tabbatar da duk masu yin burodi suna samar da burodin da ya dace da nau’i da kuma ma’auni na bai ɗaya don kare hakkin masu amfani da burodin.
-Samar da daidaito Farashi: Yin la’akari da farashi da ba da shawarar dabaru masu yuwuwa don rage farashin biredi a duk faɗin jihar.
-Kalubalen da ke shafar samar da burodi: Gano da warware mahimman batutuwan da ke kawo cikas ga bunƙasa da ingancin masana’antar burodi.
-Tsafta: A tilasta bin ka’idojin tsafta da tsaftar muhalli na duk gidajen burodin don kiyaye lafiyar jama’a.
-Yin Rijista: Tilasta yin rijista da Hukumomi, wato a tabbatar cewa duk gidajen burodin suna da rajista tare da hukumomin gwamnati da hukumomin da abin ya shafa don samar da burodi mai kyau.
– Samar da Cikakken Ƙididdiga na Gidagen Burodi / Bakery: Haɗa cikakkun bayanai na zamani na duk gidajen burodin da ke aiki a cikin jihar don samar da sauƙaƙe tsari na bai ɗaya.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
A Iya Karanta Wanna:NNPCL: Zai koma aikin haƙar ɗanyen Mai a Arewacin Najeriya
Jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar kasuwanci, Muhd Nura Yusuf, ya ce kwamitin ya ƙunshi wakilai daga ƙungiyar masu yin burodi, da ƙungiyar ci gaban kasuwar singa, da majalisar kare masu amfani da kayayyaki, da kuma babban mai ba gwamna shawara na musamman kan bunkasar tattalin arziki, wanda ya wakilci ma’aikatar zuba jari, kasuwanci, masana’antu da hadin gwiwa. Kuma ana sa ran kwamitin zai kammala aikinsa tare da mika rahoto cikin mako guda.




























