Connect with us

Hi, what are you looking for?

KASUWANCI

IMF Ta Ce Bata Da Hannu A Janye Tallafin Man Fetur A Nijeriya

oil
oil

…Ta Shawarci gwamnatin Tinubu ta samar da hanyoyin saukaka rayuwa

Daga SA K/Naisa

Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya bayyana cewa, ba shi da hannu a matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na janye tallafin man fetur a ƙasar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke zargin IMF da hannu a janye tallafin man fetur ɗin.

Gidan radiyo rFi ya ruwaito Darektan IMF a yankin Afrika, Abebe Selassie ya bayyana hakan a ranar Juma’at da ta gabata a birnin Washington DC ga manema labarai.

Ya ce matakin shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye tallafin man a matsayin batu na cikin gida ne babu hannun.

A Iya Karanta Wanna:Sojojin Isra’ila sun yi tutsu

“Matakin na cikin gida ne. Ba mu da wani shiri a Najeriya. Rawar da muke takawa ta taƙaita ne kan tattaunawa a kai a kai, kamar yadda muke yi da sauran ƙasashe irinsu Japan ko kuma Birtaniya.” Inji Selassie.

Kodayake Selassie ya bayyana cewa, matakin na gwamnatin Najeriya kan janye tallafin man na da nasaba da manufofinta na dogon-zango domin haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasar.

IMF ta ce ta lura da irin ƙuncin rayuwar da ƴan Najeriya suka faɗa sakamakon janye tallafin, tana mai shawartar gwamnatin Tinubu da ta samar da hanyoyin rage wa al’umma raɗaɗi.

Shugaba Tinubu ya janye tallafin ne jim kaɗan da shan rantsuwar kama aiki a watan Mayun bara bayan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar.

A Iya Karanta Wanna:NAHCON: Abdullahi Saleh Ya Samu Nasarar Tantance Wa A Majalisar Dattawa Don Zama Shugaban Hukumar

Jim kaɗan da janye tallafin ne, farashin litar mai da sauraren kayayyaki ya yi tashin goron zabbi a sassan ƙasar.

Har yanzu dai ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa kan yadda ake sayar da lita mai a kan naira dubu 1,200 duk kuwa da cewa shugaba Tinubu ya karɓi ƙasar a lokacin da ake sayar da lita a kan naira 200 daga tsohon shugaban Kasar Muhammadu Buhari.

← Back

Thank you for your response. ✨

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...