Akalla sojojin Isra’ila130 sun rubuta wasika da ke nuna alamun tutsu ga gwamnatin kasar cewar ba za su ci gaba da yaki ba, muddin hukumomin kasar ba za su dauki matakin kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su tun daga ranar 7 ga watan Oktobar bara ba.
Read also: Amnesty ta zargi sojojin Najeriya da yin kisan gilla a yankin Kudu maso Gabas
Gidan Radiyon Faransa ya rawaito cewar sojojin na Isra’ila a wata wasikar da suka rubuta ta ranar 9 ga wannan wata na oktoba, sojojin da wadanda aka kira domin yiwa kasar yaki sun ce sun fahimci gwamnatin kasar ba ta son kawo karshen yakin domin gudanar da zabe.
Karanta wannan:
Rukakken Dandaba Burakita Ya Gamu Da Fushin Jama’a Yana Tsaka Da Kwaccen Waya A Kano
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Daya daga cikin sojojin ya ce tun da babu wani ci gaba wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, saboda haka babu dalilin ci gaba da wannan yakin da kasar ke yi.
Sojan ya ce wannan wani matsayi ne da ya dauka na bijirewa gwamnatin kasarsa saboda yadda ta kai matakin karshe na yaudara.
Sojan ya ce da da gaske ake yi wajen kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su, da tintini anyi nasara, amma ana tsawaita yakin ne domin kin gudanar da zabe, matakin da zai bai wa (firaminista) damar ci gaba da zama a karagar mulki.
Rahotanni sun ce wasikar ta harzuka gwamnati wadda ta dakatar da wasu daga cikin sojojin.
Read also: MAJALISAR DOKOKIN JIHAR BAUCHI TA SAURARI RA’AYOYIN JAMA’A GAME DA KIRKIRO SABBIN MASARAUTU
📷 Reuters




























