Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

“Na Fasa Auren Yar Guda”, In ji Mai Wushirya

Tiktokers
Tiktokers

“Na Fasa Auren Yar Guda”, In ji Mai Wushirya
By Sunusi K/Na’isa

A yayin da kwana uku rak da wata kotun Majistare ta ba da umarni ga fitaccen ɗan TikTok, Ashiru Idris wanda aka fi sani da Mai Wushirya ya auri Yar Guda a kwana 60, sakamakon samun su da yaɗa baɗala a kafafen sada zumunta wanda ya sabawa al’ada da addini a jihar kano. A yanzu da alama an yanka ta tashi, domin kuwa Mai wushirya ya ce ya fasa auren Basira Yar Guda.

” Na janye auren Yar Guda, dama bin umarnin kotu zan yi, yanzu kuma na fasa auren”. Mai wushirya ya ke faɗa a wani sabon fefan bidiyo da ya wallafa a kafar sada zumunta a yau.

A sabon bidiyo da Mai Wushirya ya fitar, ya bayyana cewa duba da ƙorafe-ƙorafen da iyayensa suka yi da sauran abokansa, yana shaida wa mutane cewa idan ya tashi aure zai sanar da su lokaci da rana da kuma wadda zai aura.

Makamancin Labarin:Kotu ta Umarci Masu Barkwanci Na TikTok A Kano Dasu Yi Aure Bayan Yaɗa Bidiyon “Futsara”

Ya ƙara jaddada cewa da ma ba a son ransa ya amsa cewa zai auri ’yar Guda ba, tsoro ne na hukuncin kotu.

Dan wasan ya yi kira ga duk waɗanda suka karɓi kuɗin gudunmawa da sunan wannan biki da su miƙa kuɗin ga mabuƙata da marayu.

Idan za a tuna, wata Kotu a Kano ƙarƙashin alkalancin Mai Shari’a Majistare Halima Wali ta umarci Mai wushirya da Yar Guda dasu tabbatar sun yi aure kafin ko zuwa kwana 60 bisa sanya ido ga hukumar Hisbah ta Jiha domin tabbatar da auren.

Jaridar The Stentor News, ta ruwaito labarin da Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta ƙasa, Mr. Mazi Afam Osigwe, SAN, ya soki hukuncin Mai Shari’a Halima Wali, ya ce babu wani hurumi a kundin tsarin mulkin ƙasa da ya bada damar a tilastawa wani ko wasu su auri juna ba tare da yardar su ba. Don haka ya ja hankalin kotun ta sake duba game da hukuncin.

A saboda haka al’umma suke ganin ko Mai wushirya yayi wukar kugu da wanna sanarwar ta shugabannin Lauyoyi ne ta ƙasa ko kuma ta makaho yake, wai an ce a yi wasan jifa?

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...