Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Magidanci Mai Mata 2 Ya Kashe Ɗan Achaɓa Don Samun Kuɗin Ƙarin Aure

Kwamishina Yan Sanda na jihar Bauchi Sani Omolori Aliyu
Kwamishina Yan Sanda na jihar Bauchi Sani Omolori Aliyu

Magidanci Mai Mata 2 Ya Kashe Ɗan Achaɓa Don Samun Kuɗin Ƙarin Aure

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi ta kama wani magidanci mai Sana’ar sayar da kayan marmari a Bauchi, saboda kashe dan acaba tare da ɗauke mashin ɗinsa don ya sayar ya samu kuɗin biyan sadakin ƙara auren mata ta uku.

Rundunar Ƴan sanda ta sanar da kama mutumin mai suna Mamuda Zakaria Yau, mai shekaru 30 a duniya bisa zargin sa da caka wuƙa wa Basiru Mohammed mai shekaru 25 a duniya wanda ya ke sana’ar achaɓa a cikin garin Bauchi.
Kamar yadda wanda ake zargin da aikata laifin ya shaidawa ‘Yan sanda cewa ya hau achaɓa daga shataletalen dogon yaro zuwa bayan tsohon Airport a kan naira 600. amma da suka je wajen da babu mutane sai ya burma masa wuƙa ya hau mashin ɗin ya kara wuta.

Jami’in hulda da Jama’a na Rundunar yan ‘sandan jihar Bauchi CSP Ahmad Muhammad Wakil a nasa ƙarin bayani cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce a ranar Alhamis 16/10/2025 da misalin karfe 9 na dare wani mai suna Mahmud Zakari Yau, mai shekaru 30 a duniya sun yi sa-in-sa da wani mai suna Basiru Mohammed da yake sana’ar achaɓa wadda ya fito daga yankin Zango Sa’idawa, a yayin sa-in-sar, shi Ya’u an zargin ya yi amfani da wuƙa ya caka wa Mohammed Dan acaba tare da yin awan gaba da babur ɗinsa kirar Bajaj launin Ja, mai lamba NNG813UM. Sai ko da aka yi sa’a Mohammed ya nemi ɗaukin mutane ta hanyar ihu, yadda maƙwabta suka kawo masa agaji tare da bin wanda ake zargin, hakan ya tilasta masa jefar da Babur ɗin, ya ranta cikin na Kare.

Ga Wani Makamancin Labarin:Yan Sanda Sun Kama Wanda Ya ƙwaƙule Idon Kanwar Sa Da Kuma Bokan Da Ya bashi Sa’ar

Bayanin ya ƙara da cewa Jami’an Yan sanda daga ofishin su dake Yelwa cikin hanzari sun isa wajen tare da ɗaukar wadda aka caka wa wuƙar zuwa Asibitin koyarwa na ATBUTH, inda likitoci suka bayyana cewa ya rasu.

CSP Ahmad Wakil ya ƙara da cewa an ajiye gawar a Asibiti don kammala bincike da gwaje-gwaje.
Kuma biyo bayan bincike an cafke wanda ake zargin ta hanyar bayanai da aka samu a cikin wayarsa da ya jefar da rigarsa mai ɗauke da wasu kayayyaki a cikin aljihun.

Yan sanda sun kira wasu lambobin mutane da yayi waya da su aka sanar da su cewa ya samu hatsari yana asibiti su zo. Da suka zo don kawo masa ɗauki aka cafke su aka je inda yake aka kama shi.
Kuma a lokacin da ake tuhumarsa ya amsa laifinsa, inda ya alaƙanta yin kisan da cewa sharrin shaiɗan ne, DA kuma tsananin rashin kuɗin ƙara mata ta uku, da hakan ya sa shi yaudarar Ɗan Achaɓan tare da caka masa wuƙa ya ɗauke mashin nasa don ya sayar ya samu kuɗin sadakin auren matar da ya yi mata alƙawarin zai aure ta, amma abin da yake samu a sana’ar sa ta sayar da kayan marmari bata wadatar da shi yadda zai samu kuɗin cikawa matar alƙawarin auren da ya yi mata ba.
Kakakin Rundunar Yan Sanda CSP Mohammed Ahmed Wakil ya ce an samu shaida a wajen da suka haɗar da Babur Bajaj Boxer da wuƙa mai jini a jiki da Takalmi da wayar Salula ta wadda ake zargin.

Ga Wani Makamancin Labarin:Jita-Jitar Juyin Mulki Ba Gaskiya Bane Kuma Makirci Ne — Shelkwatar Tsaro

Kwamishinan Ƴansanda na Jihar, CP Sani- Omolori Aliyu ya bada umarni a maida binciken zuwa Sashen binciken manyan laifuka na CID don ƙara bincike tare da gabatar da mai laifin gaban Kotu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...