Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Fiye da Musulmi Miliyan Uku Sun Hallara a Katsina don Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse

Mauludin Sheikh Ibrahim Inyas
Mauludin Sheikh Ibrahim Inyas

Fiye da Musulmi Miliyan Uku Sun Hallara a Katsina don Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse

Daga Sunusi K/ Naisa

Fiye da Musulmi miliyan uku daga sassan Najeriya da wasu ƙasashen Afirka sun hallara a Jihar Katsina domin tunawa da Mauludi (ranar haihuwa) na marigayi jagoran darika Tijjaniyya, Sheikh Ibrahim Niasse.

An gudanar da taron addinin na tsawon mako guda a filin wasa na Dukko Radda, Katsina, ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Majma’u Ahbab Niasse. Taron ya ja hankalin manyan malamai na addinin Musulunci, sarakunan gargajiya, da dubban mabiya darikar Tijjaniyya daga jihohi 36 na Najeriya da ƙasashen Yammacin Afirka.

An Kama Umar Da Wasu Matasa 2 Da Ake Zargi da Kashe Matar Aure Da ‘Ya’yenta 6 A Kano

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Ƙungiyar Majma’u Ahbab Niasse, Sheikh Ahmad Tijjani Sani Auwal, ya ce bikin Mauludin na shekarar 2026 ya cika shekaru 40 da fara gudanar da shi a kowace shekara. Ya bayyana cewa an shirya taron ne domin girmama rayuwa da koyarwar Sheikh Ibrahim Niasse, tare da yin addu’o’i na zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki a Jihar Katsina, yankin Arewa maso Yamma da kuma Najeriya baki ɗaya.

Sheikh Auwal, wanda kuma shi ne Kwamishinan Ma’aikatar Harkokin Addini ta Jihar Kano, ya bayyana cewa wannan ne karo na uku da Katsina ke karɓar bakuncin Mauludin, bayan wanda aka gudanar a shekarun 2002 da 2016. Ya ƙara da cewa jihohi irin su Zamfara, Sakkwato da Kebbi ma sun taɓa karɓar bakuncin irin wannan taro a baya.

Shalkwatar Tsaron Nigeriya Ta Bara Kan Harin Kaduna

Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Katsina bisa samar da yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali da ya ba da damar gudanar da taron cikin nasara, tare da yin addu’ar dorewar zaman lafiya da haɗin kai a jihar da ƙasa baki ɗaya.

A nasa jawabin, Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya yi kira ga haɗin kai a tsakanin mabiya darikar Tijjaniyya da kuma al’ummar Musulmi gaba ɗaya. Ya haskaka gudunmawa gami da tarihi da Sheikh Ibrahim Niasse ya taka wajen yaɗa Musulunci a fadin Afirka, inda ya bayyana shi a matsayin babban malami mai tasiri wanda ilimisa ya wuce iyakokin ƙasashe.

A ɓangaren sa, Gwamnan Jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda, ya nuna godiya ga masu shirya taron bisa zaɓar Katsina a matsayin jihar da ta karɓi baƙunci. Ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tallafa wa ayyukan addini da ke inganta zaman lafiya, haɗin kai da daidaituwar al’umma, tare da kira da a ci gaba da yi wa Najeriya addu’a.

Manyan baƙi daga Najeriya da ƙasashen Yammacin Afirka sun halarci taron, ciki har da wakilan Babban Sakataren Ƙungiyar Haɗin Kan Musulunci (OIC),  kuma Khalifa Sheikh Mahi Sheikh Ibrahim Niasse, wanda Muhammad Qurash Sheikh Ibrahim Niasse daga Senegal ya wakilta.

Mauludin, wanda ya fara tun daga ranar Lahadi ya ɗauki tsawon kwanaki bakwai, wanda aka kammala a ranar Asabar da karatun Alƙur’ani mai girma, addu’o’i, wa’azin addini da taruka na ilimi, dukkansu don haskaka rayuwar koyarwa da  tarihi na fitaccen jagoran Tijjaniyya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...