Al’ummar Sabuwar Gandu Sun Karrama Alh. Muktar Aliyu Custom da Walima Girmamawa Bayan Kammala Shekaru 35 Na Aiki
Daga Wakilinmu
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Kafatanin Al’ummar Unguwar Sabuwar Gandu dake jihar Kano da maƙotansu sun yi fitar ɗango zuwa wajen walimar taya ɗan su, na Allah mutumin Allah, gwarzo abin koyi Alh Muktar Aliyu bisa kammala aikin gwamnati shekara 35 lafiya a Hukumar Hana Fasa ƙwari ta kasa (Custom).
Taron ya gudana a ranar Alhamis 1st January 2025, a ɗakin taro na Ali Jita Even Center dake kan titin Lawan Dambazau Road Kano, ƙarƙashin jagorancin Dr Ibrahim Muhammad Gandu, da Alhaji Anas tare da Abdullahi Abubakar Bisi da sauran yan kwamatin dattawan unguwar Sabuwar Gandu.
Allah ya albarkaci taron da iyayen ƙasa hakimai da masu unguwanni da mutane masu dajara da manyan abokanan aikin sa.
An haifi Alhaji Mukhtar Aliyu a Gandun Sarki wato (Audu Bako Secretariat) ta yanzu a shekarar 1969. Ya fara neman iliminsa na addini tun yana dan shekara 3, a makarantar marigayi Malam Danyaro.
A lokacin da ya tasa aka saka shi a makarantar boko ta Gandun Nassarawa Furamare a shekarar 1977 zuwa 1982. Daga nan ne tafiya ta neman ilimi ta fara nisa, inda ya sami sa’ar shiga Karamar Sakandare ta Sabuwar Kofa a shekarar 1982 zuwa 1985. Daga nan ne ya rubuta jarabawar shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha, ya sami shiga Government Technical College Kano a shekarar 1985 zuwa 1988, inda ya kamala da samun Takardar Shaida ta Kwarewa a Fannin Ilmin Gyaran Lantarki (Electrician).
Bayan kammala wannan karatu ne ya sami aiki cikin ikon Allah a Hukumar Kwastam Ta Kasa a shekarar 1991, a matsayin Mataimakin Kwastam mai matsayi na III. Daga nan ya tafi Makarantar Horon Aikin Kwastam dake Kano, a inda suka sami Horo na wata 6.
Bayan kammala wannan aikin Horo ne aka tura shi Jihar Katsina da aiki. Bayan ya shafe tsawon shekara 3 a Jihar Katsina ne sai ya sami canjin wurin aiki, a inda aka dawo da shi Jihar Kano a shekarar 1996, yayi aiki ne a Malam Aminu Kano International Airport.
Read also: Gobe Litinin Ita Ce 1 Ga Watan Rabi’ul Awwal, 1447 bayan hijira, In ji Sarkin Musulmi
Yanayin aiki ya sa an sake canza masa wurin aiki a shekarar 1999, inda aka tura shi aikin zuwa Jihar Port Harcourt. Bayan ya shafe shekara 3 a can, sai aka sake tura shi Jihar Enugu a shekara ta 2002.
Ya yi aiki na tsawon shekara 2 a Enugu, kafin daga bisani aka mayar da shi babbar Shalkwatarsu ta Kasa da ke Abuja a shekarar 2004. Ya shafe shekara 4 a Shalkwata, kafin daga nan aka sake tura Jihar Lagos, a inda ya yi aiki dangaren Lagos, Tincon to Kano /Jigawa Area Command.
A shekara ta 2002 bayan ya koma Abuja, sai ya yanke shawarar komawa Makaranta, a inda ya sami amincewar Shugaban da yake aiki a karkashinsa, kasancewar a lokacin yana da takardar Shaidar Karatu da ya yi a fannin Electrician. A nan ne ya nemi shawara daga Malam Ibrahim Mohammed Gandu, ya ba shi shawarar komawa karatu a FCE, Kano, inda ya yi karatu a bangaren gudanarwa Certificate of Administration (CA).
Ya sami Takardar Karatu a kangaren Gudanarwa, bai tsaya da neman ilimi ba, sai da ya sake komawa Kwalejin Fasaha ta Kano, inda ya sami Karama (ND) da Babbar Takarda Diploma Ta Kasa a fannin Kasuwanci da Tattalin Arziki (HND) a tsakanin shekarun 2006 zuwa 2009.
Bayan kammala wannan karatu ne a shekarar 2009 ya yi Jarabawar neman Karin Matsayi, inda ya sami Karin girma zuwa Assistant Supretendant II (ASC II). Daga nan tafiya ta ci gaba, inda a shekarar 2013, ya sake zuwa Jarawa ta neman karin matsayi zuwa Assistant Supretendant I (ASCI).
A cikin shekarar 2013 ne bayan ya sami karin girma likkafa ta sake dagawa, aka zabe shi zuwa Sashen Customs Inteligent Unit. Ya je Lagos kwas na wata 3. Bayan ya kamala kwas din ne aka tura Lagos Sashen SAPID. Dagan an ne aka sake dawo da shi Kano, a shekara ta 2017 cikin ikon Allah ya sake samun ci gaban matsayi zuwa matakin Deputy Supretendant (DSC).
A matakin shekara ajiye aiki ne Allah ya sake daga shi zuwa mukamin Supretendant of Custom (SC), matsayin da Allah ya nufe shi da ajiye aiki a kai.
Custom mutum ne na kwarai da nagarta da son cigaban al’umma a duk inda ya sami kansa, Allah ya albarkaceshi da dukiya irin wadda Allah yake so, domin gwanine wajen taimakawa al’umma da wannan dukiyar tasa.
Kyautata Zamantakewar Aure: Kungiyar Anwarul-Qalam Bauchi ta Horas da ‘Yan Mata 100
Read also: Daliban Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil sun Karrama Shugaban Hukumar Karota
Babban abin alfahari da shi wannan bawan Allah din shine, wallahi bai dauki kansa a kamai ba, ko wani mai kuɗi, yana da ladabi da biyayya ga kaskantar da kai daga na sama da shi har zuwa na kasa da shi.
Ƙungiyar ‘yan jaridu na yanar gizo -gizo ta jihar Kano na taya murna ga Alhaji Muntari da iyalansa murnar kammala aiki lafiya.




























