Kungiyar Ci gaban Kampala Sun Cirawa Sanata Ahmed Tagiya Saboda Fitar Dasu Daga Matsanancin Duhu
Daga Wakilinmu
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Read also: HUKUMAR ICPC TA GURFANAR DA LIKITAN NASIRU ELRUFAI A GABAN KOTU
Shugaban Kungiyar ci gaban unguwar kampala, Kampala Development Forum (KDF), ya yaba da kuma godiya a madadin al’ummar unguwar Kampala ga Sanatan Jinkan al’umma, Sanata Ahmed Abdulhamid Mallam Madori, mai wakilta Jigawa ta Gabas, dake jihar Jigawa a Nijeriya bisa yaye musu matsanancin duhu dake addabar su.
Shugaban Kungiyar ci gaban unguwar Kampala, Maiunguwa Ibrahim Zakar Ibrahim (Al-kampaly) shi ya sanar da haka da yake zantawa da kafar yada labarai ta STENTORNEWS, ya ce godiyar ta zama wajibi ga Sanata Ahmed, saboda share musu hawaye da yayi a cikin kwanaki kadan wajen kawo musu injina bada wutar lantarki wato (Transformer) na milyoyin kudi domin magance matsalar da ta addabi al’umma mazauna unguwar shekara da shekaru.
A Karanta Wanna:Akalla Mutane 20 Sun Hallaka Ya Yin Da Suke Tserewa Farmakin ‘Yan Bindiga a Zamfara
“Maigirma Sanata, mazauna kampala, manyan da yara mata da maza nayi ma addu’a ga Allah Subahanahu Watala da ya kara arziki ya kareka daga sharrin mahassada”. Inji Shugaba Ibrahim.
Daga bisani kungiyar ci gaban unguwar Kampala, (KDF) sun roki sauran masu rike da madafun iko da su yi koyi da Sanata Ahmed Mallam Madori, domin samun ci gaba cikin hanzari.
A Karanta Wanna:Rungumar Sana’a Ce Mafita Ga Matasa, In Ji Pharm. Sule
Kamar yada ya ce rashin wutar lantarkin ya tauye ci gaban yankin, ta fuskar tattalin arziki da kyautata rayuwar mazauna unguwar, musamman ga masu kananun sana’o’i dake da alaka da wutar lantarkin. Amma a halin yanzu komai ya inganta kamar yadda Maiunguwa ya shaidawa Wakilin kafar yada labarai ta STENTORNEWS.
Unguwanni da suka sami tagomashin Sanata Ahmed, sun haɗar da Ungugwar Kampala da Unguwar Dunari da kuma Kofar Fada a inda ko wacce aka bata Taransifomar guda dai-dai.




























