Majalisar Shari’ar Najeriya Ta Nemi Tinubu Ya Cire Shugaban INEC Saboda Wani Rubutu Mai Cike da Cece-kuce Akan “Kisan Kare Dangi”
Daga Wakilinmu
Read also: China Na Goyon Bayan Shugaba Tinubu, Kuma Tayi Tur Da Barazanar Trump Ga Najeriya
Majalisar Kolin Shari’ar Musulunci ta Najeriya (SCSN) ta bukaci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya kori sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, saboda zarginsa da rubuta wata mukala mai cike da cece-kuce a shekarar 2020. Majalisar ta bayyana cewa, takardar, wadda ta sake bayyana a kwanan nan, ta ƙunshi kalmomi masu tayar da hankali da son rai da kuma abin da zai iya lalata haɗin kan ƙasa.
Wannan takarda da ake magana a kai mai taken “Legal Brief: Genocide in Nigeria – The Implications for the International Community” an wallafa ta ne ta ƙungiyar International Committee on Nigeria (ICON), wata ƙungiya da aka fi sani da ta fafutukar kare ’yancin addini. Rahoton, tare da wani da ya yi kama da shi mai taken “Nigeria’s Silent Slaughter,” ya zargi hukumomin Najeriya da rashin kulawa da hare-haren da ake kaiwa kan Kiristoci da ƙananan ƙabilu.
Majalisar Shari’ar ba ta amince da abubuwan da ke cikin wannan takarda ba, tana cewa ta kawo labarin da babu ko kanshin gaskiya a ciki, waɗanda suka nuna Musulmai a Arewacin Najeriya a matsayin masu aikata kisan kare dangi. Ta ce wannan zargi abin damuwa ne musamman idan aka yi la’akari da cewa mutumin da ake magana a kai yanzu shi ne ke da alhakin jagorantar tsarin zaɓen ƙasar.
Read also: MAJALISAR DOKOKIN JIHAR BAUCHI TA SAURARI RA’AYOYIN JAMA’A GAME DA KIRKIRO SABBIN MASARAUTU
Haka zalika, Majalisar ta bayyana cewa bayanan da ake zargin Farfesa Amupitan ya yi ba su dace ba kuma Abin takaici ne ace daga gareshi suka fito ba duba da matsayin ilimin da da matsayin da yake kai ba, kuma tabbas kalaman suna barazana ga haɗin kai da zaman lafiya da kwanciyar hankali na Najeriya. Ta jaddada cewa shugabantar zaɓe a ƙasa mai addinai daban-daban na bukatar nuna adalci da rashin son rai, abin da rubuce-rubucen da ya gabata na Farfesa Amupitan ba su nuna hakan ba.
Majalisar ta ƙara da cewa tashin hankali a Arewa da Arewa ta Tsakiya yana shafar dukkan al’ummomi Musulmai da Kiristoci baki ɗaya, ba tare da laifin wata ƙungiya ko addini guda ɗaya ba.
Majalisar ta ce rikice-rikicen yankuna sun samo asali ne daga abubuwa masu yawa kamar ta’addanci da ’yan fashi da talauci, da halin ko in kula da gwamnati tayi na tsahon lokaci.
Ta kuma kawo rahotannin alkaluma na yan agaji da ke nuna cewa Musulmai ne suka fi yawa cikin waɗanda ke rasa rayukansu a jihohin Arewa da dama kamar Borno da Zamfara da Katsina da Sokoto da kuma Yobe. Don haka majalisar ta soki ƙoƙarin da ake yi na danganta rikice-rikicen wannan lokaci da jihadin Sheikh Uthman ɗan Fodio na ƙarni na 19, tana cewa hakan na nufin ɓata tarihi da samar da rarrabuwar kawuna a ƙasa.
Majalisar ta bayyana cewa kuskure ne fassara Jihadin Sokoto a matsayin yaƙin ƙiyayya haka kuma babban abin kunya ne, domin manufarsa ta asali ita ce gyara da samar da adalci, da yaduwar ilimi. Ta ce irin wannan ƙage bai kamata ace ya fito daga shugaba da ake sa ran zai tabbatar da gaskiya da sahihancin zaɓe ba.
Read also: Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar
China Na Goyon Bayan Shugaba Tinubu, Kuma Tayi Tur Da Barazanar Trump Ga Najeriya
Saboda haka, Majalisar Shari’ar ta roƙi Shugaba Tinubu da ya sake duba naɗin Farfesa Amupitan tare da janye shi domin kare haɗin kan ƙasa da samar da ingantaccen tsarin zaɓe. Ta kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya ba tare da tayar da rikicin addini ba, tana mai jaddada cewa abokan gaba ƙasar nan sune rashin adalci da cin hanci da talauci da rashin tsaro. Majalisar ta sake tabbatar da ƙudirin ta na ƙarfafa zaman lafiya da gaskiya da mutunta juna tsakanin mabambantan addinai.(Politics Nigeria)





























Pingback: INEC: Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Ƙasa Na Zaɓen Shekarar 2027 - The StentorNews Hausa