China Na Goyon Bayan Shugaba Tinubu, Kuma Tayi Tur Da Barazanar Trump Ga Najeriya
Daga Sunusi K/Naisa
Gwamnatin ƙasar Sin (China) ta yi gargadi ga Amurka kan duk wani yunƙuri na tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Najeriya, hakan ya biyo bayan barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na amfani da ƙarfin soji don hukunta Najeriya kan zargin cin zarafin masu addinin Kiristanci.
Read also: Shugaba Donald Trump Ya Soke Visa Dubu 80 Ta ‘Yan Najeriya Da Wasu Kasashen Waje
A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Talata nan, Mao Ning, mai magana da yawun Ma’aikatar harkokin wajen China, ya bayyana cewa Beijing “na goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu gaba ɗaya wajen tafiyar da al’amuran Najeriya a kan hanya madaidaiciya da ci gaba.”
Read also: Ban taɓa cin haram ba a shekaru 35 a aikin Gwamnati a Najeriya, in ji Barista Mainasara Kogo
Mao ya kara da cewa:” Sin, a matsayin ta na abokiyar haɗin gwiwa, tana adawa da duk wata ƙasa da ke amfani da addini ko hujjar kare haƙƙin ɗan adam wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gida, ko yin barazanar takunkumi ko amfani da ƙarfin soji.”
Wannan martani na China ya biyo bayan yamutsa hazo da maganganun Shugaba Trump na Amurka suka haifar a faɗin Afirka da sauran sassan duniya, inda ƙasashe da dama suka yi Allah wadai da kalaman Trum na barazanar Amurka domin tsoratar da ƙasa Najeriya.




























