Amurka Na Yunƙurin ƙaƙabawa Gwamnonin Arewacin Najeriya 12 da Alƙalai da Sarakunan Gargajiya Takukumi
Daga Edita
Amurka ta fara wani gagarumin yunƙuri na saka takunkumi a kan gwamnonin arewa 12 da manyan alkalai da fitattun sarakunan gargajiya a Najeriya kan zargin tauye ’yancin addini da abin da wasu ’yan majalisar Amurka suka kira “kisan kiyashin Kiristoci” a Arewa.
Wannan mataki dai na da nasaba da ƙaruwar damuwa a Washington kan batun ’yancin addini da kuma yadda dokokin Shari’a da na batanci ke aiki a wasu jihohin Arewacin Najeriya.
A cewar wasu ’yan majalisar Amurka, mutanen da ake shirin hukuntawa sune waɗanda suka yi biris da hare-haren da ake kai wa Kiristoci da sauran ƙananan ƙabilu da addinai.
Ana gabatar da wannan yunƙuri ne ƙarƙashin wani ƙudiri da ke neman a hukunta manyan jami’an gwamnati da ake zargi da ƙarfafa ko goyon bayan bambancin addini.
Idan aka amince da ƙudirin, takunkumin zai haɗar da hana su shiga ƙasar Amurka da hanasu tasarafi da dukiyar su da ke Amurka da kuma takunkumi ƙarƙashin tsarin kare haƙƙin ɗan adam na duniya na Amurka.
China Na Goyon Bayan Shugaba Tinubu, Kuma Tayi Tur Da Barazanar Trump Ga Najeriya
Wannan lamari ya biyo bayan kalaman da tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, inda ya ce an kashe dubban Kiristoci a Najeriya, kuma dole Amurka ta ɗauki mataki cikin hanzari. Ya ce za a binciki lamarin tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu “ba tare da ɓata lokaci ba.”
A cikin ƙudirin akwai a bin da ake kira dokar Yancin gudanar da addini da kuma tsentseni ta Najeriya ta shekarar 2025, (Nigeria Religious Freedom Accountability Act of 2025) da Sanata Ted Cruz ya gabatar. Kudirin zai sanya Najeriya cikin jerin “ƙasashen da ke da matsala ta musamman,” tare da neman hukunta jami’an da suke “goyon bayan dokokin batanci.”
Kudirin ya kuma buƙaci a sa ido kan jihohin da dokokin Shari’a ke aiki.
Read also: BASHI NA DAF DA DURKUSAR DA NAJERIYA
Jihohin da lamarin ya shafa sun haɗa da: Zamfara da Kano da Sokoto da Katsina da Bauchi da Borno. Sauran su ne Jigawa da Kebbi da Yobe da Kaduna da Niger da kuma jihar Gombe. Sai dai jihohin Kwara, Kogi da Plateau daBenue, Nasarawa daTaraba, da Adamawa suna bin tsarin doka ta zamani kawai, inda Shari’a ta tsaya ga batutuwan aure da gado kawai.
Masu suka kan ƙundin sun ce Amurka na sauƙaƙa batun tsaro mai matuƙar rikitarwa.
Jami’an Najeriya sun ƙaryata zargin cewa ana nuna wariyar addini ga Kiristoci, inda suka ce matsalolin tsaro a Arewa sun fi nasaba da ta’addanci, ’yan fashi da sauran miyagu laifuffuka ba tare da alaƙa da tsarin mulki ko na addini ba.
Gwamnati ta ce Shari’a na aiki ne kawai ga Musulmi, kuma kotunan tarayya na da ikon rushe hukuncin Shari’a idan ya saba wa kundin tsarin mulki.
Tashin hankali kan batun ya ƙaru bayan Amurka ta yi barazanar dakatar da tallafi har ma ta nuna yiwuwar kai farmaki da ƙarfin soji zarar zargin kisan Kiristoci bai tsaya haka ba.
Wani babban jami’in Amurka ya kuma yi iƙirarin cewa Amurka “za ta kashe ’yan ta’addan Islama” idan Najeriya ta gaza kare Kiristoci.
Fadar Shugaban Ƙasar Najeriya ta tabbatar cewa Shugaba Bola Tinubu zai gana da Donald Trump nan ba da jimawa ba don tattaunawa kan zargin tare da ƙarfafa haɗin gwiwa kan yaƙi da ta’addanci. Jami’an gwamnati sun ce tattaunawar za ta fayyace gaskiya tare da tabbatar wa Amurka sahihan bayanai kan tashin hankali a Najeriya.
Masu nazari kan harkokin diflomasiyya da tsaro sun yi gargaɗi cewa takunkumin zai haɗar da samar da kayan yaƙi ga Najeriya daga Amurka da musayar bayanan sirri da tallafin ƙasashen waje.
‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Gami Da Garkuwa Da Wasu A Kano
Sun kuma ce wajibi ne Najeriya ta magance matsalolin da suka shafi kashe-kashen gungun mutane da rikicin addini da raunin aiwatar da hukunci kan laifukan batanci.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Sai dai wasu sun jaddada cewa duka Musulmi da Kiristoci a Najeriya suna fuskantar hare-haren ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Idan za a tuna a watan Mayu na shekara 2022, aka kashe Deborah Samuel a Sokoto kan zargin batanci wanda ya tayar da jijiyoyin wuya a faɗin ƙasar da wajen ta, wanda ya sa aka yi kira da a ƙarfafa dokokin kariya da gaggauta hukunta masu aikata laifukan tashin hankali da suka shafi addini on ji yan majalisar.
politicsnigeria.com




























