Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Gobara ta ƙone Gidan Tsohon Gwamnan a Abuja ƙurmus

Gobara
Gobara

Gobara ta ƙone Gidan Tsohon Gwamnan a Abuja ƙurmus

Daga Yazid Sunusi Yahaya

Wata gobara da ta tashi a ranar Asabar ta lalata gidaje huɗu daga cikin biyar na gidajen kwana masu ɗakuna uku da ke kan titin Nelson Mandela, Asokoro, Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta fara ne daga na’urorin hasken rana (solar panels) da aka girka a saman rufin ɗaya daga cikin gine-ginen, kafin ta bazu zuwa sauran gidajen da ke kusa.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, Shugabar Hulɗa da Jama’a ta Sashen Kula da Bala’o’i na Tarayya (FEMD), Nkechi Isa, ta ce kadarar da abin ya shafa mallakin tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, Sanata Ahmed Yerima.

Ƙirƙirar Hisbah Mai Zaman Kanta A Kano Ya Saɓawa Doka, In Ji Farfesa Mai Bushira

Isa, tana ambaton Shugaban Tawagar Bincike da Ceto ta FEMD, Monday Addie, ta ce an samu rahoton lamarin ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana a ranar Asabar.

“Ba a rasa rai ko guda ba a wannan gobara. Sai dai gidaje huɗu daga cikin biyar sun ƙone ƙurmus,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa an lalata kayayyakin amfanin gida da dama, ciki har da kayan ɗaki, tufafi, kayan abinci da sauran muhimman kayayyakin gida.

Rungumar Tsarin Majalisar Wuccin Gadi A Najeriya Na Iya Ajiye Biliyoyin Naira A Shekara, In Ji Ali Ndume

Jami’an agaji daga FEMD, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Hukumar Kashe Gobara ta FCT, Hukumar Kula da Bala’o’i ta Ƙasa (NEMA), da Rundunar ’Yan Sandan FCT sun kai ɗauki wurin, inda suka samu nasarar shawo kan gobarara

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...