Gobara : Kasuwar Ƴan Katako A Kano Ta Kama da Wuta
By Sunusi K /Naisa
Read also: Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
Gobara ta lakume dukiya da asubahin wannan rana ta Laraba, a kasuwar ’yan katako da ke Rijiyar Lemo a jihar Kano, lamarin da ya jawo fargaba a yankin.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Ana Zargin Batagarin Matasa Da Bankawa Dubban Kaburbura Wuta A Makabartar Turum Dake Bauchi
Wutar ta shafi wasu rumfuna tare da haddasa asarar kayayyaki, amma ba a samu bayanin rashin rai ba.
Read also: Gobara Ta Kone Gidaje, Na’urar Wutar Lantarki a Kano
Jami`an kashe gobara da al’ummar yankin ne suka kai ɗauki cikin gaggawa, inda suka yi nasarar shawo kan gobarar kafin ta bazu.
Wazirin Ningi Ya Yi Murabus, Sakamakon Tsoma Siyasa a Harkokin Masarautar Ningi
Har ya zuwa yanzu babu cikakken alƙalima na yawan dukiyar da a ka rasa.
Idan za a tuna a makon da ya gabata aka samu makamancin hakan na tashin gobara a kasuwar Singa, ɗaya daga cikin manyan kasuwanni dake a jihar Kano. Tuni Gwamna Kano Alh Abba Kabir Yusuf ya bawa ‘yan kasuwar Singar gudunmawar Naira Miliyan 100 tare da alƙawarin gina manyan hanyoyin mota.



























