Ƙungiyar RATTAWU Na Ta’aziyya Ga Gwamna Abba Yusuf Bisa Rashin Hazziƙan ‘Yan Majalisa Ungogo da KMC
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: Kano: An Soke Dokar Da Ta Kafa Hukumar KNUPDA – Majalisar Dokoki
Ƙungiyar Ma’aikatan Radio da Talbijin da Raya Al’adu ta Ƙasa reshen Jahar Kano (RATTAWU), ta aike da sakon ta’aziyya ga Maigirma Gwamnan Jihar Kano Alh. Abba kabir Yusuf da Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi II da Shugaban Majalissar dokoki na Jahar Kano Rt. Hon. Isma”ila Falgore da iyalan ‘yan majalissun ƙananan Hukumomin Ungogo da Ƙaramar Hukumar Birni da suka rasu a ranar Larabar data gabata.
Read also: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Amince da Karin Girma ga Malaman Makaranta 16,634.
NIN Yanzu Zai Aiki a Matsayin TIN ga Mutane, Hukumar Haraji ta Tarayya Ta Sanar da Hakan
Shugaban ƙungiyar RATTAWU reshen jihar Kano, Comrade Babangida Mamuda Buyamusu ya miƙa sakon Ta’aziyya ga kafaffan yaɗa labarai.
Read also: Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Dongwarar da Jam’iyyar NNPP
Buyamusu, ya ce jihar Kano na alhakin rashin waɗannan masa aikin Majalisa da kuma taimakon al’ummar yankunan su, ya bayyan rashin amtsayin babban rashi ga al’ummar Jihar Kano dama ƙasa baki ɗaya, inda yai addu’ar Allah ya gafartamusu yasa aljanna makomarsu.
Hon. Aminu Sa’ad Ungogo da Hon. Sarki Aliyu Daneji sun rasu a ranar Laraba da ta gabata, sakamakon rashin lafiya.



























