Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Rundunar Yansanda Jihar Kano Ta Ce Fefan Bidion Da Ake Yaɗawa Na Barawo Ali Kwara Tsoho Ne Shekaru 6 Da Suka Gabata

Kwamishina Yan sanda jihar Kano
Kwamishina Yan sanda jihar Kano

Rundunar Yansanda Jihar Kano Ta Ce Fefan Bidion Da Ake Yaɗawa Na Barawo Ali Kwara Tsoho Ne Shekara 6 Da Ya Gabata

Daga Sunusi K/Naisa

Rundunar Ƴansanda ta jihar Kano ta ce bidiyon da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na cewa an kama wani da ake kira “Ali Kwara” ba sabon bidiyo ba ne, sai dai wani bidiyo ne na ganawar manema labarai da aka yi tun a shekarar 2019 a hedkwatar Ƴansanda, Bompai.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Ƴansandan Kano, rundunar ta ce an kama mutumin a 2019 a Diga, Panshekara, bisa zargin sace-sace da fashi da makami, inda ya amsa laifinsa a lokacin bincike. Bidiyon, in ji rundunar, wani bangare ne na bayanin da aka yi wa jama’a kan kokarin yaki da laifuka a wancan lokaci.

Rundunar ta yi kira ga jama’a da su guji yaɗa bidiyoyi ko bayanai marasa tushe da ka iya jefa jama’a cikin tsoro ko tayar da hankula.

Nambobin Wayar Kar-Ta-Kwana Daga Hukumar Yan Sandan Jihar Kano

Ta kuma tabbatar da cewa tana ci gaba da sa ido domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da rokon jama’a da su rika tantance bayanai kafin yadawa.

Babbar Kotun Tarayya Abuja ta yanke hukunci ga wanda ya kitsa munanan hare-hare a Kano

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya gode wa jama’a bisa haɗin kai wajen bayar da bayanai da ke taimakawa wajen tabbatar da tsaro a Kano

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...