Rundunar Ƴan sanda ta Hana Goyo a Babur a Kano
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano ta sabunta haramcin ɗaukar fasinja a kan babura, tare da takaita zirga-zirgar adaidaita sahu daga ƙarfe 10 na dare zuwa 6 na safe a wasu kananan hukumomi.
Dokar, wacce gwamnatin jihar ta kafa a baya, ta shafi Kano Municipal da Gwale da Dala da Fagge da Nassarawa da Tarauni da Kumbotso da Ungogo (yanki na Jido) da Dawakin Kudu (Tambuwal, Gurjiya da Jido Ward).
Read also: Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Kwamishinan ‘Yansandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya gargaɗi masu babura da adaidaita sahu da su bi doka, inda ya ce duk wanda aka kama yana karya doka zai fuskanci fushin hukuma.
Haka kuma, rundunar ta buƙaci jama’a da su hanzarta kai rahotan duk wani abu da ka iya barazana da tsaro ta hanyar layukan gaggawa na ‘yan sanda.
Read also: Rundunar Yan Sanda Sun Bankado Shirin Kona Gidan Gwamnatin Jihar Kano
Sanarwar da kakakin rundunar ƴansandan, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta bayyana cewa jami’an ‘yansanda da na KAROTA zasu tabbatar da abin dokar.



























