Masu Zanga-zanga sun ƙone Fadar Sarki da ofishin hukumar NDLEA ƙurmus a jihar Kwara
Daga Sani Aminu
Read also: Hukumar NDLEA ta Gano Maboyar Miyagun Kwayoyi a Ƙarƙashin Ƙasa a Kano
Mazauna garin Lafiagi da ke ƙaramar hukumar Edu a jihar Kwara sun fito kan tituna a ranar Litinin ɗin da ta gabata don nuna rashin amincewarsu da abin da suka bayyana da tabarbarewar tsaro a yankunan su da suka haɗa da ta’addanci da sace-sace da kashe-kashe.
Masu zanga-zangar waɗanda galibansu matasa ne daga yankin, sun bayyana rashin jin daɗinsu kan abin da suka kira gazawar gwamnati wajen fuskantar tashe tashen hankulan.
An dai gansu a cikin wani faifan bidiyo suna rera waƙoƙin haɗin kai da kuma daga allunan nuna goyon baya, inda suka bukaci a kawo ɗauki cikin gaggawa domin daƙile zubar da jini da sace-sacen mutane da ke kawo cikas ga rayuwar yau da kullum. Matasan da suka fusata sun ƙona ofishin hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA da ke Lafiagi tare da lalata fadar Sarkin Lafiagi tare da farfasa tagogi da kuma lalata sassan ginin.
A karanta:Shugaban ‘Yan Bindiga Bello Turji Na yunƙurin Miƙa Wuya Bayan Mutuwar Yelo Danbokolo
“Muna kuka muna mutuwa shiru,” in ji wani mazaunin a cikin faifan bidiyon. “Ana sace mutane kowane mako, ba ma kwana da idanu biyu a rufe, kuma ba kowa, ko gwamna, da shugaban ƙasa, ko ma sarki da ke yin komai a kai.”
Read also: Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano
Majiyoyin sun ce zanga-zangar ta samo asali ne sakamakon yawaitar hare-haren da ake ci gaba da kaiwa da kuma rashin ɗaukar ƙwararan matakai daga hukumomin ƙananan hukumomi da jihohi. “Matasan sun gaji, kuma babu wani ƙwaƙƙwaran mataki da gwamnati ta ɗauka,” inji wata majiya. “Yawancin hare-hare ya ƙaru a kai a kai da ya sa zanga-zangar ta barke a yau.”
Rahotanni sun ce tarzomar ta yi ƙamari ne yayin da masu zanga-zangar suka nufi wasu muhimman gine-ginen gwamnati, ciki har da ofisoshin hukumomin tsaro. Kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana, an ƙona cibiyar NDLEA a yayin zanga-zangar.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
A karanta:Mutuwar Aminu Dantata Babban Rashi ne Ga Ƙasa Da Ma Duniya Baki Ɗaya- Gerawa
Lafiagi da al’ummomin da ke maƙwabtaka da su suna fuskantar sace-sacen mutane da dama a cikin ‘yan makonnin nan, inda har yanzu ana tsare da mutane da dama. An bayar da rahoton cewa iyalan waɗanda abin ya shafa sun biya maƙudan kuɗaɗe domin biyan kuɗin fansa don a sako ‘yan uwansu.




























