Mutuwar Aminu Dantata Babban Rashi ne Ga Ƙasa Da Ma Duniya Baki Ɗaya- Gerawa
Shugaban Rukunin Daraktocin Kanfanonin Gerawa Group, Alhaji (Dr). Ibrahim Muhammad Gerawa ya ce hakika mutuwar Alh Aminu Dantata babban rashi ne baga al’ummar kasar nan ba harma ga faɗin duniya baki ɗaya.
Read also: Ansamu Koma Bayan ‘Yancin Gudanar Da Aikin Jarida a Faɗin Duniya A Shekaru 5 – Rahoton IEAD
Sanarwar wacce ta fito ta hannun Shugaban Rukunin Daraktocin Kanfanonin amadadin Shugaban Kanfanonin Alh. Isah Muhammad Gerawa ya ce al’ummar jihar Kano na cike da damuwa bisa rashin shugaba abin koyi, attajiri mai hidima ga jama’a da kuma addinin Allah, wanda ya ce al’ummar ƙasa za su cigaba da yi masa addu’a bisa kyawawan halayensa da kuma gudunmawar da ya bawa jama’a.
Read also: Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar
A karanta:Bashi Ko Ceton Rai? Kukan zuci da Siraɗin da Ma’aikatan Gwamnati ke ciki a Nigeria
Sanarwar ta yi Kira ga attajiran ƙasar nan da suyi koyi da halin dattijo mai jin kan al’umma Alhaji Aminu AlHassan Dantata, ” Muna roƙon Allah ya gafarta masa ya kuma sa Aljanna Firdausi makoma.
Read also: Ƙungiyar Rajin Kare Hakkin Ɗan Adam ta Duniya Ta Yi Allah Wadai da Cin Zarafin Ɗan Jarida A Kano
Mataimaki na musamman akan harkokin Yada Labarai na Kamfanonuwan GERAWA Comrade Babangida Mamuda Biyamusu shi ya sa hannu tare da rabawa manema labarai a yau.




























