An Gargadi Ƴan Jaridar Yanar Gizo Da Suyi Aiki da Kwarewa Tare da Ƙare Martabar Kasa
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: “Ku Bar Ofisoshi Ko Ku Fuskanci Hukunci,” Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikatan Da Suka Kai Ritaya
Wani ɗan siyasa a Jihar Kano, Inuwa Ibrahim Waya, ya yi kira ga ‘yan jaridar yanar gizo da su rungumi ƙa’idojin aikin jarida tare da bin kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya a cikin rahotannin su na yau da kullum gami da kare martabar ƙasa.
Waya ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi ga ‘yan jarida a Kano, inda ya jaddada muhimmiyar rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen sanar da al’umma sahihin bayanai cikin gaskiya da rikon amana.
Canja Jam’iyya a Siyasar Kano Ya Zo a Kan Lokaci, Kuma Muniface Mai Kyau– Inuwa Waya
Ya bayyana cewa ‘yan jarida na taka muhimmiyar rawa wajen gina fahimtar jama’a, don haka dole ne su guji gurɓata labarai, ko labarin da zai tayar da hankali, ko duk wani rahoto da zai iya haifar da rikici tsakanin al’umma.
“Na shawarce ku da ku yi taka-tsantsan wajen yadda kuke bayar da rahotanni, musamman idan sun shafi martabar gwamnati ko mutane ko kamfanoni. Dole ne ku tabbatar da cewa rahotanninku ba su jefa ku ko wasu cikin haɗari,” in ji shi.
Read also: Sabbin Kwamishinoni Sun Karbi Rantsuwar Kama Aiki A Kano
Yace samar da ingantaccen rahoto da bincike na cikake gami da bin ka’idojin aiki shine mafita don kaucewa afkawa cikin rikici da kuma shari’a a kotuna.
Alhaji Ibrahim Waya ya kuma nuna jin daɗinsa kan shigar da Ƙungiyar ‘Yan Jaridar Yanar Gizo cikin babbar ƙungiyar ‘yan jaridu ta ƙasa (NUJ), inda ya bayyana hakan a matsayin babban mataki na ƙarfafa ƙwarewa da tsaftace sana’ar a aikin jarida.
Ya taya sabbin shugabannin ƙungiyar murna tare da ƙarfafa musu gwiwa da su rungumi ladabi da da’a da ƙwarewa wajen gudanar da ayyukansu domin samun ci gaba a jihar Kano.
Da yake waiwaye kan yadda aikin jarida ya samo asali, Waya ya lura cewa kafin zuwan kafafen yanar Gizo (online), hanyoyin yaɗa labarai na bin matakai da dama wanda hakan ke haifar da jinkiri ko karkatar da bayanai. Ya ƙara da cewa, a yanzu da kafafen yanar gizo suka bunƙasa, masu karatu na samun labarai sau da dama a rana, wani lokacin har sau 10 zuwa 20 kuma cikin hanzarin, saɓanin tsoffin hanyoyin yaɗa labarai.
Read also: ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Buƙatar Su
Ƙungiyar Rajin Kare Hakkin Ɗan Adam ta Duniya Ta Yi Allah Wadai da Cin Zarafin Ɗan Jarida A Kano
Tsohon ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar APC a Jihar Kano ya kuma tabbatar da samun haɗin kansa ga ƙungiyar domin tallafawa ƙungiyar tare da ƙarfafa martabar sana’ar.




























