Sabbin Kwamishinoni Sun Karbi Rantsuwar Kama Aiki A Kano
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: MAJALISAR DOKOKIN JIHAR BAUCHI TA SAURARI RA’AYOYIN JAMA’A GAME DA KIRKIRO SABBIN MASARAUTU
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabbin Kwamishinoni tare da sanar da su ma’aikatun da zasu gudanar da aiki a jihar.
Barr. Abdulkarim Kabir Maude shi ne Kwamishina Shari’a a kuma babban lauyan gwamnatin jihar Kano.
Haka kuma gwamnan ya rantsar da Dr. Aliyu Isa Aliyu a matsayin Kwamishina a sabuwar Ma’aikatar Bunkasa Al’amuran Kiwon Dabbobi.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
Ga Wani Labarin:Cire Kwamishinan ‘yansandan Kano tamkar kashe maciji ne ba’a sare kan ba.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma rantsar da Barr. Salisu Muhammad Tahir a matsayin Babban Sakatare a Ma’aikatar Sharia ta jiha.
Da yake rantsar da sabbin kwamishinonin a yayin zaman majalisar zartarwa karo na 32, gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira gare su dasu zamo masu gaskiya da rikon amana a yayin gudanar da ayyukan su.
Ya ce nadin nasu an yi shi ne bisa cancanta la’akari da gogewa da kwarewar su da kuma irin gudummawar da suke bawa al’umar jihar Kano a fannoni daban-daban.
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Ga Wani Labarin:Bauchi: Ƙungiyar Fulani Sullubawa Sun Yi Alwashin Samar Da Haɗin Kai Don Ingantaccen Tsaro
Ya taya sabbin kwamishinonin murna tare da fatan zasu bada gudummawa wajen bunkasa cigaban jihar Kano.




























