Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Bauchi: Ƙungiyar Fulani Sullubawa Sun Yi Alwashin Samar Da Haɗin Kai Don Ingantaccen Tsaro

Jihar Bauchi
Jihar Bauchi

Bauchi

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Ganin yadda ƙabilar Fulani ke fiskantar ƙalubale da dama game da zamantakewa da tattalin arziki da tsaro a Najeriya, ƙungiyar Fulani sullubawa reshen jihar Bauchi ta gudanar da taronta na jiha don bayyana matsayin ta game da neman ingancin zaman lafiya a kowane sashe a Nageriya da kasashen Afirka.
Sarkin Sullubawan jihar Bauchi Alhaji Dr. Ibrahim Waziri, masani kan harkar sadarwar zamani shine ya jagoranci gudanar da taron a dakin taro na fadar Sarkin Bauchi Dr Rilwanu Sulaiman Adamu don hada kan Fulani sullubawa da ke zaune a sassan jihar Bauchi.
Cikin jawabinsa Dr. Ibrahim Waziri bayyana matsayin sa na dan kasa mai kishi da son zaman lafiya da haɗa kan Fulani don magance matsalar da suke fiskanta wacce ta shafi duk ta’addanci da laifuffuka idan an aikata ake samun Fulani a ciki, ko Kuma a gefe guda basu san hawa ko sauka ba idan an aikata laifin ake ɗora musu.

Ga Wani Labarin:Gwamna Yusuf Ya Ce Majalisar Shura Ta Duba Koken Ƙungiyoyin Addini, Game Da Lafazin Malam Lawan Triumph
Don haka ya nuna godiya ga fadar maimartaba Sarkin Bauchi saboda ba shi Sarautar Sarkin Sullubawan jihar Bauchi.
Dr Ibrahim Waziri a karon farko ya bayyana cewa ya karbi wannan sarauta ce saboda tausayin Fulani musamnan sullubawa don ganin yadda ake cin zarafin su tare da kashe su ba tare da hakkin su ba.
Sarkin ya danganta rufe kan iyakoki da gwamnati ta yi tun daga kan ƙasar Sakkwato da kewayen ta na daga cikin sanadin da ya haifar da matsanancin talauci da rashin aikin yi.
Hakan ya sa da yawa wasu sun sa son zuciya tare da faɗawa cikin aikata miyagun laifuffuka, daga bisani Fulani masu zaune da dukiyar su, sun bar yankin zuwa neman tudun tsira amma duk yadda suka je ana tsangwamar su.
Ya Ƙara da cewa Fulani masu arziki ne, kuma akan arzikin su ake faɗa da su ake zaluntar su. Don haka ya bukaci Fulani su kasançe masu hakuri da bin doka, a sannu ƙungiyar za ta bi musu haƙƙi kan dukkan abin da ke faruwa, musamnan ya shirya gabatar da ƙararaki kusan biyar da ya ke son shigarwa don bin haƙƙin ‘yan Najeriya musamnan Fulani.
Shugaban ƙungiyar Fulani Sullubawa ta jihar Bauchi Alhaji Mohammed Abubakar da Alhaji Nasiru Garba Aminu Magayakin Bauchi da Alhaji Abubakar Usman suna cikin manyan baki da suka gabatar da jawabai a wajen taron, yadda suka ja hankalin Fulani sullubawa game da zaman lafiya tare da neman filayen zama don kiwon shanun su da kuma yin gonaki don noma abinci.
Suka ce sakacin iyaye Fulani Sullubawa wajen mallakar gonaki da filin gidajen zama shi ya haifar da matsalar da ake fiskanta a halin yanzu saboda ƙasa ta yi daraja duk ‘yan kasuwa da yan siyasa sun karɓe dazuka sun mayar dasu gonaki.
Alhaji Abubakar Usman da Aliyu umar da Adamu Sarkin Fadar Badaromo, cikin jawabinsu na neman haɗa kai da kuma ƙoƙarin su na ganin an tuntubi gwamnatin jihar Bauchi don cika ƙudirin Gwamna Bala Mohammed Abdulƙadir na bin haƙƙin Fulani don samun zaman lafiya.
Don haka a shirye suke wajen ganin ƙungiyar ta kafu don a samun shiga jikin gwamnatin Sanata Bala Mohammed domin a tabbatar da ƙudirin sa na farfaɗo da labin shanu da filin kiwo da gyara burtali, kuma sun bukaci Fulani su kai yaran su makaranta.
Alhaji Abubakar Mohammed daga yankin Dindima yace sun fi shekara 40 a yankin amma tun da suke basu mallaki filaye ba, amma yanzu ana neman korar su daga filayen gwamnati saboda ƙasa ta yi daraja.
Don haka ya ce ƙungiya na bukatar kudi da lokaci domin samun gudanar da ayyukan ta kamar yadda ya dace gami da tafiya da murya guda.

Ga Wani Labarin:Dambatta Ta Ba Sabbin Malamai Tallafin Naira Miliyan Ɗaya
Daga ƙarshen taron an bayyana sunan shugabannin yankuna da ƙananan hukumomi, Kuma an bukaci kowane mutum da ya kai shekara 18 ya fito don yin katin jefa guri’a. Haka kuma an bukaci kowa ya rika yin rijistar yaran sa a asibiti ta hanyar zuwa awo da aihuwa a asibitocin gwamnati don Karba wa yara katin ɗan ƙasa a duk yadda ake don gudun maimaita kussakurai da Fulani suka yi a baya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...