Gwamna Yusuf Ya Ce Majalisar Shura Ta Duba Koken Ƙungiyoyin Addini, Game Da Lafazin Malam Lawan Triumph
Daga Adita
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta karɓi koke-koke da ƙorafe-ƙorafe daga ƙungiyoyin addini kan kalaman da Sheikh Lawan Triumph ya yi a kwanan nan kan fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallahu Alahi Wasallam.
Read also: One Kano Agenda: Gwamna Yusuf Ya Nuna Samun Haɗin Kai Shine Mabuɗin Farfaɗo da Jihar Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ba da umarnin a miƙa batun ga Majalisar Shura ta Jiha domin ta yi nazari tare da ba da shawarwari game da batun.
Mai magana da yawun ofishin Sakataren Gwamnati na Jiha, Musa Tanko, ya bayyana cewa kungiyoyin da suka shigar da korafin sun haɗa da Safiyatul Islam of Nigeria da Kungiyar Wayar da Kan Matasa ta Tijjaniyya,da Interfaith Parties for Peace and Development, da Sairul Qalbi Foundation da Habbullah Mateen Foundation da Limaman Masallatan Juma’a na Qadiriyya da Kwamitin Malaman Sunnah Kano da kuma Multaqa Ahbab Alsufiyya.
Sakataren Gwamnati na Jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya tabbatar da cewa gwamnati ta mika batun ne domin a yi masa cikakken nazari da kuma bayar da shawarwarin da suka dace.
Ga Wani Labarin:Dambatta Ta Ba Sabbin Malamai Tallafin Naira Miliyan Ɗaya
Read also: Ɗan Jarida Zai Gurfanar da Hadimin Gwamna Kano a Kotu, Sakamakon Zargin Cin Zarafi
Ya ce gwamnati na da cikakken niyyar tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai da mutunta juna tsakanin kungiyoyin addini a jihar.
“Mun yi kira ga jama’ar Kano da su kwantar da hankali, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum tare da bin doka da oda,” in ji shi.
Idan za a tuna a ranar laraba ne wasu matasa sukayi zanga zanga kan furucin malamin akan Fiyayyen halitta Manzon tsira Annabi Muhammad SAW da suka ce kalaman sun yi tsauri.
Daga nan gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya karbi korafin matasan yace su rubuta a miƙa wa ofishin Sakataren gwamnatin jiha.
Read also: Gwamna Inuwa Yahaya Ya Kaɗu Matuƙa Da Rasuwar Ƴan Jarida Sakamakon Hatsarin Mota
Ga Wani Labarin:Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantun 8 masu zaman kansu
Sai dai a safiyar Alhamis ɗinna Malaman Ahalussunnah karkashin jagorancin Dr. Abdullah Gadon Kaya, suma sun miƙa nasu koken cewa Malamin yana kan daidai kuma suna bukatar ayi adalci.




























