Dambatta Ta Ba Sabbin Malamai Tallafin Naira Miliyan Ɗaya
Daga Tasi’u Jibo Dawanau
Majalisar Ƙaramar Hukumar Dambatta ta bada tallafin Naira Miliyan Ɗaya (₦1,000,000) ga sabbin malamai da aka ɗauka aiki a yankin, domin ƙarfafa musu gwiwa da kuma ƙara musu ƙaimi wajen aiwatar da aikinsu.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Ga Wani Labarin:Kotu Ta Tabbatarwa ICPC Damar Bincikar Zargin Badaƙalar Tallafin Karatu A Kano
Read also: Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Malam Mador / Kaugama Ya Raba Tallafin Karatu Ga Ɗalibai 500
Kamar yadda aka sani, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya raba takardun ɗaukar aiki ga fiye da malamai 4,000 a fadin jihar, a wani yunkuri na inganta ayyukan ilimi.
Da yake jawabi yayin rabon takardun tura su wuraren aikinsu a sakatariyar ƙaramar hukumar da ke garin Dambatta, Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar Dambatta, Alhaji Jamilu Abubakar Dambatta, ya jaddada muhimmancin ladabi da jajircewa wajen koyarwa.
Read also: Karamar Hukumar Ghari Ta Raba Takardun Daukar Aiki Ga Malamai 50
Ga wai Labarin:Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantun 8 masu zaman kansu
Ya kuma ja hankalin malamai da su rika zuwa aiki da wuri, su kasance masu gaskiya da biyayya domin ganin ci gaban ilimi ya samu a cikin gaggawa.




























