An Nemi a Gyara Auran Matasan Da Sukai Aure Akan Sadaki ₦3000, A Maimakon Dauri
Daga Muazu Hardawa Bauchi
Wani mahaifin ango da aka ɗaurawa aure akan sadakin Naira ₦3000 ba kuma tare da waliyan ko wanne bangare ba, walau Amarya ko kuma Ango ya roki Uwargidan Gwamna Bauchi domin ta sanya baki don a gyara auren bisa tsari na shari’ar Musulunci maimakon a kaisu gidan gyaran halin.
Read also: Ana Zargin Batagarin Matasa Da Bankawa Dubban Kaburbura Wuta A Makabartar Turum Dake Bauchi
Idan za a tuna mun kawo muku labarin yadda ‘Yan sanda a jihar Bauchi ke tsare da wasu matasa bakwai da suka haɗar da Ango Muhammad Chindo da Amarya mai suna Kamila da abokan su da suka shaida ɗaura auren a kan sadakin naira dubu Uku.
Rikicin wannan aure ya ɗauki salo kala-kala lamarin da ya sa Jami’an ƙungiyar Sintiri ta Alhaji Umar Shayi vigilante suka yi dirar mikiya a unguwar Mahaukata da ke Bauchi cikin dare suka kama angon da amarya da abokan sa, suka tsare su na kwanaki biyu a ofishin su da ke Inkil a Bauchi.
Hukumar NDLEA ta Gano Maboyar Miyagun Kwayoyi a Ƙarƙashin Ƙasa a Kano
Wakilinmu ya ziyarci ofishin hukumar Shari’a yadda ya zanta da shugaba Dr. Hamisu da Kwamishina Hisbah Bar. Aminu Balarabe Isah yadda suka ce sun samu labarin faruwar auren da kamen da mutanen Umar Shayi suka yi. Kuma sun buƙaci a kawo musu yaran don su daidaita lamarin ko kuma su kai su ga ƴan sanda.
Amma sunce wannan batu ne mai sauƙi da za su iya gyarawa don basa son a riƙa kai matasa gidan gyaran tarbiyya ko ofishin Yan sanda saboda kada su ɗauki miyagun halayen da suka fi wanda suke aikatawa.
Mun tuntubi Jamiin Hulda da jamaa na Umar Shayi Malam Abdullah Isah ya tabbatar da kama yaran kuma sun tsare su yace suna bincike kan lamarin za su miƙa su hukumar da ta dace.
Read also: EFCC Ta Kori Ma’aikata Sama da 40, Ta Gurfanar da Biyar Kan Cin Hanci da Rashawa
Haka kuma jaridar The Stentor Hausa, ta tuntubi kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi SP Nafiu Habib ya ce an kawo yaran zuwa ofishin su na Township Bauchi ana tsare da su domin ci gaba da bincike nan bada jimawa ba za a yi abin da ya dace.
A gefe guda uwargidan gwamnan jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Mohammed ta Kira taron gaggawa na manema labarai da Sarakunan gargajiya a karkashin kwamitin ofishin ta na yaƙi da cin zarafin jinsi, ta nuna damuwa game da yadda irin waɗannan matsalolin ke faruwa kuma ta roƙi iyaye su riƙa lura da rayuwar ‘ya’yensu da gyaran tarbiyya ta hanyar sanya ido a kan su.
Don haka ta bukaci sarakuna da Malaman addini da fastoci da Yan jarida su ci gaba da ƙoƙarin wayar da kan jama’a game da gyara halin matasa.
Malam Abdullahi wanda shi ne mahaifin ga Ayuba Abdullahi ɗaya daga cikin matasan da ake tsare da su bisa zargin aikata laifin ya bayyana cewa an kama yaronsa ne a gidan sa cikin dare yau kwana biyar saboda ya halarci wajen auren a zaman sa na aboki ɗan unguwa da suka taso tare da angon.
Don haka ya roƙi uwargidan gwamnan Hajiya Aisha Bala Mohammed ta taimaka ta sa baki a bayar da belin su kuma ta bada sadakin da ya dace wanda ya Kai rubuu dinare don a gyara auren da yaran suka daura tsakanin Mohammed Chindo dan kimanin shekara 25 da Kamila Shehu yar kimanin shekara 20.
Kuma ya roƙi da ta taimaka ta shiga cikin lamarin su da na sauran yaran a taimaka musu wajen daura musu aure da ‘yan matan da suke so. Saboda akasarin matasan da aka kama kowa yana da budurwa kuma sun Kai aure amma talauci ya hana su yin auren.
Don haka yake zargin wannan dalili shi ya sanya matasan fito da sabon salon kulla aure da wanda suke so ta kowane hali.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Sojoji Sun Dakile Harin Lakurawa, Sun Kwato Makamai da Ceto Dabbobi 62
Malam Abdullahi ya bukaci uwargidan gwamnan ta taimaka kamar yadda ake yi a ofishin Hisbah na Kano tasa a zakulo wasu matasa a haɗa da waɗannan ai musu aure da tallafin gwamnati idan ta yi haka Allah zai bata lada kuma ta taimaki yaran da iyayen su. Saboda Kai irin waɗannan matasa gidan yari ba zai haifar da ɗa mai ido ba.




























