Gwamnatin Kano Ta Yaba da Nadin Shugabannin Gidajen Rediyo Bisa Cancanta
Daga Sunusi K/Na’isa
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta taya murna tare da jin daɗin nadin sabbin shugabannin wasu manyan gidajen rediyo guda huɗu da ke cikin jihar.
Read also: “Ku Bar Ofisoshi Ko Ku Fuskanci Hukunci,” Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikatan Da Suka Kai Ritaya
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida ta fitar, gwamnatin ta bayyana jin daɗinta tare da miƙa sakon taya murna ga waɗanda aka nada, a madadin gwamnatin da al’ummar jihar Kano.
Ga Wani Labarin:ICPC Ta Kama Dan Jaridar Bisa Zargin Damfara Ta Naira Miliyoyin 14
Read also: Tsohon ma’aikacin gidan rediyo Kano, Malam Ali Sufi Utai, ya rasu
Waɗanda aka naɗa su ne:
– Anas Idris Hassan, Janar Manajan , Vision FM Radio Kano
– Garba Ubale Dambatta, Janar Manajan, Pyramid FM Radio Kano
– Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu, Janar Manajan, Nasara FM Radio Kano
– Muhammad Musa Mohammed Inya, Janar Darakta, Hikima FM Radio Kano
Sanarwar ta bayyana cewa naɗin nasu ya samu ne bisa cancanta da nagarta, inda kowannensu ya ke da ƙwarewa da hazaka, da kuma sadaukarwa a fagen aikin jarida tsawon shekaru.
Read also: Rashin Bin Ƙa’idar Gini, Gwamnatin Kano Ta Rusa Dogon Bene A Nassarawa GRA
Ga Wani Labarin:BARAYI SUN GUNTULE HANNUN MATASHI A JIHAR KEBBI
Gwamnatin ta kara da cewa tana da tabbacin cewa sabbin shugabannin za su taka rawar wajen bunƙasa harkokin yaɗa labarai a Jihar Kano. Tare da bada tabbacin tafiya tare da gwamnati domin isar da sako ga al’ummar jihar Kano.




























