Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Addu’ar Magabata ita ce Sirin Samun Zaman Lafiya a Mararabar Gurku, Inji Sarkin Hausawa Mani

Sarkin Hausawa Mararaba Alh Adamu Usman Mani
Sarkin Hausawa Mararaba Alh Adamu Usman Mani

Sarkin Hausawa 

By Sunusi Kofarnaisa

Sarkin Hausawa Mararaba Gurku, da ke Karamar Hukumar Karu a Jihar Nassarawa a Arewacin Nijeriya Alhaji Usman Adamu Mani, ya ce addu’ar magabata da kuma kaunar baki su ne siri na bunkasar garin.

Alhaji Adamu Mani ya sanar da haka da yake zantawa da wakilin jaridar Stentornews a fadar sa dake garin na Mararaba a ranar Lahadi.

Sarkin Hausawa ya ce dama-chan Mararaba gari ne mai tarihi da ya yi shuhura wajen karbar baki da kuma samun zaman lafiya. Shugaban al’ummar ya nunar ce wa duk da garin yana kunshe da jinsin kabilu daban-dabam da yare kala-kala ga kuma addinai mabambanta, waɗanda manya daga cikinsu, su ne na addini Musulimci da Kiristanci amma bai hana kowa ya gudanar da ibadar sa ba duk da cewa shugaban sarakuna Esu Karu Mai bin addinin kiristanci ne amma yana bawa kowa damansa. Mararaba ba a taba wayar gari cikin tashin hankali ba duk da rigingimun da ake yi a wasu sassa na arewa a Nijeriya.

A Karanta Wanna:DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)

Sarki Mani, ya jaddada kudirin masarautarsa na ci gaba da samun kyakkyawan zamantakewa tsakanin al’ummar domin samu ci gaba mai ɗorewa, inda ya ce babu wata al’umma da za ta ci gaba ta hanyar tashin hankali da samun rashin kyakkyawan zaman lafiya.

IMG 20250303 WA0012

” Idan ka duba garin Mararabar Karu bai wuce shekaru hamsin da kafuwa ba, ita sarautar Sarkin Hausawa kuma,  akalla za ta kai sama da shekara 20, amma ci gaban yankin ya darawa sa’arta a fanin ci gaba da kuma bunkasa kasuwanci”.

Da yake magana ga tarihin nadin sarautar sa Alhaji Usman Mani, ya ce yin Allah ne, domin a farko baya daga cikin ‘yan takarar neman sarautar, amma daga bisani Allah ya bashi bisa amincewar shugaban sarakuna, Sarki Esu Karu, ya nemi ya zama daga cikin ‘yan takara.

Alhaji Usman Mani, ya nuna godiyar sa ga Allah da kuma mutanen da yake mulka wadanda su ne ginshikin kasancewarsa Sarkin Hausawa Mararaba bayan gushewar sarautar Sarkin Hausawa Muhammad Damaturu da kuma Ali plamber.

Basaraken wanda nan da ‘yan watanni masu zuwa zai cika shekaru biyar da nadawa a gadon mulki, a matsayin Sarkin Hausawa na Mararaba Gurku, ya ce ya gamu da kalubale kala-kala, musamman daka al’ummar sa da suka fito daga jihar Katsina, amma cikin yardar Allah abin ya zamo tarihi.

A Karanta Wanna:Wani Shaida Ya Ce Ya Biya kuɗin Fansa Miliyan N80 Ga Tukur Mamu Domin Fansar Mahaifiyarsa da Kanwarsa

Alh. Usman Mani, ya ce a yanzu haka masarautar sa na gogayya da sauran masarautu na hausawa, wanda a yanzu

” Duk lokacin shagalin bikin sallah mukan yi hawa domin nuna farin ciki ga wanna rana”. Haka kuma muna haɗa kan al’ummar Hausawa mazauna garin tare da yin sulhu na aure ko cinikayya ko makwabtaka da sauran su batare da an je gaban Alkali ba, baya ga bada gudunmawa ta kowace fuska idan ta taso”. Inji Usman Mani.

” A yanzu a gaban ka, ka tarar muna kokarin daidaita ‘yan uwa, waɗanda rashin aiwatar da rabon gadon mahaifin su akan lokaci ya nemi ya haddasa fitina a tsakanin su, toh irin wadannan na kadan daga cikin ayyukan mu”.

A Karanta Wanna:Wani Sanata A Nijeriya Ya ce Sun San Manyan Hafsoshin Sojan Da Suke Hakar Ma’adanai Babu Izini

Daga bisani Alhaji Adamu Usman Mani, ya yi addu’ar samun ci gaban garin na Mararaba da karin samun kwanciyar hankali da yalwar arziki mai ɗorewa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...