Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Gwamnatin Tarayya Haɗin Gwiwa da Bauchi Sun Samar da Motocin Daukar Marasa Lafiya Kyauta

Bauchi Ambulance
Bauchi Ambulance

Gwamnatin Tarayya Haɗin Gwiwa da Bauchi Sun Samar da Motocin Daukar Marasa Lafiya Kyauta

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Ganin yadda majinyata marasa karfi ke fuskantar matsalar zuwa asibiti musamnan a cikin dare, gwamnatin tarayya da hadin guiwar gwamnatin jihar Bauchi sun fito da Wani shiri na musamnan don dauko marasa lafiya daga gida zuwa asibiti.

Shirin zai yi aiki tsawon awa 24 wato dare da rana, kuma tuni aka buɗe ofis tare da tanadar motocin ɗaukar marasa lafiyar, suna jiran kiran ko ta kwana daga masu bukatar taimakon gaggawa.

A Karanta Wanna:An Yi Jana’izar Hanshakin Basarake Galadiman Kano Abbas Sunusi
Professor Abdulkarim Mairiga shugaban asibitin kwararru na Bauchi da ke BACAS cikin zantawarsa da wakilinmu a lokacin fara kaddamar da Shirin, ya ce kowane majinyaci ko Yan uwansa za su iya kiran lambar 112, ko 07033064032, motar zata zo ta ɗauki majinyacin, musamnan idan ciwon ya zo masa a gaggauce kuma ba shi da halin zuwa asibiti a kan lokaci. Kuma duk Wanda aka dauko za ai masa jinya da magani kyauta tsawon awa 24 kafin ‘yan uwansa su shirya su ci gaba da jinya.

Dr. Mairiga Abdulkarim yace an tanade magungunan ko-ta-kwana da dukkan kayan jinyar taimakon gaggawa da za a yi aiki da su domin bayar da taimakon gaggawa ga majinyacin kyauta.

Shima shugaban Shirin na Ambulance Dr Sulaiman Abubakar wanda shine Daraktan magance yaɗuwar cututtuka a ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Bauchi ya ce wannan shirin an jima da fara gudanar da shi a wasu jihohin Nigeria. Don haka yanzu suka himmatu don ganin ya iso Bauchi domin talakawa su ci moriyar don rage wahala ko raguwar muce-mace da marasa galihu ke yi.

A Karanta Wanna:Galadiman Kano Abbas Sunusi ya Rasu

Da zarar an kira wannan lambar za a gaggauta ɗauko marasa lafiya a kai zuwa daya daga cikin asibitoci biyar da aka tanada don aiwatar da shirin. Yace mutane za su amfana karkashin shirin don an tanada manyan ambulance da magunguna da likitoci na musamnan don ci gaban shirin. Kuma ana Shirin samar da karin lambobin waya a kowane sashi don amsa kiran ɗauko majinyatan zuwa asibiti.

A Karanta Wanna:Asiri Ya Tonu: Saura Kiris Wayar Salula ta Haɗa Auren da Babu Wali Ba Siga

Bayan haka Dr. Abubakar ya kara da cewa akwai yiwuwar faɗaɗa shirin zuwa kananan hukumomi 20 na jihar Bauchi tare da samar da wasu motocin ambulance da za a ci gaba da aiwatar da shirin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...