Connect with us

Hi, what are you looking for?

Kotu

Asiri Ya Tonu: Saura Kiris Wayar Salula ta Haɗa Auren da Babu Wali Ba Siga

Wayar Salula
Wayar Salula

Asiri Ya Tonu: Saura Kiris Wayar Salula ta Haɗa Auren da Babu Wali Ba Siga

Daga Wakilinmu

Allah ya toni asirin wasu matasa da sukai ƙoƙarin shirya aure ba tare da sanin Wali ko wakili ba, bale kuma sigar aure daga liman a unguwar Alkalawa, Karamar Hukumar Kura dake jihar Kano.

Wakilinmu ya ruwaito cewa wani abin ban mamaki kuma wayar salula da ba ta wuce dubu 40 ba kachal ita ce tai sanadin kulla auren domin an nemi ta zama a matsayin sadaki.

Jami’an Hukumar Hisba na Karamar Hukumar Kura su sukai ram da matasan biyu, waɗanda suka haɗar da Yusuf Akilu Hamisu me shekara 30, wanda a kai ikirarin shi ne angon, da kuma Farouk Lawan Yusuf, wanda ya ke a matsayin waliyin amarya.

A karanta Wanna:Sanata Natasha ta Dura A Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu A Kogi, Duk da Gargadin Jami’en Tsaro

Sai dai kuma abin al’ajabi, babu dangin iya babu na baba.” Lokaci guda kurum su ka kirkiri auren domin ya zamar musu abin nishadi, kamar yadda amaryar gan-gan ɗin Sadiya Isa, ‘yar shekara 24, ta faɗawa jami’an Hisba”, ta ce dukkaninsu mazauna unguwar Alkalawa ne da ke yankin karamar hukumar Kura a Jihar Kano.

A ranar Talatar da ta gabata ne dakarun na hisba suka kai sumame gurin da ake shirye-shiryen bikin bayan samun bayanan sirri.

A halin da ake ciki, tuni shugaban Hukumar Hisba a karamar Hukumar Kura, Ustaz Ali Alkassim Kura ya sanar da al’amarin ga shugabancin karamar hukumar, karkashin jagorancin Alh. Rabiu Abubakar Suleiman Babina, wanda tuni ya bayar da umarnin gudanar da bincike tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Bayan kammala bincike, an gurfanar da su a kotun shariar musulunci da ke zamanta a Garun Malam.

A karanta Wanna:Galadiman Kano Abbas Sunusi ya Rasu

Al’kalin kotun ya tuhume su da aikata laifi da ake zargin sun aikata, amma sun musanta hakan. Daga bisani Alkalin kotun ya bayar da belinsu sannan ya dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Afrilun na shekarar da muke ciki.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...