Connect with us

Hi, what are you looking for?

Siyasa

Sanata Natasha ta Dura A Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu A Kogi, Duk da Gargadin Jami’en Tsaro

Natasha Akpoti
Natasha Akpoti

Sanata Natasha ta Isa Kogi a Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu, Duk da Gargadin Jami’en Tsaro na Hana ta jirin gwana motoci.

Daga Adita

Jama’ar Kogi sun fito kwai da kwarkwata gabadaya domin tarbar wakiliyar su a Majalisar Dattijai ta Kogi ta tsakiya Santa Natasha Hadiza Jimoh Audu Akpoti.

Sanatar ta Sauka a Jirgin Sama wato Helikofta duk da hana ta tafiya da ayarin mota da hukumomi su kai.

Sanatar ta sauka sanye da farin gyade cikin fara’a ga jama’ar ta.

A Karanta Wanna:Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Da take jawabi Sanatar ta sha alwashin ” Ba wanda zai hana ni zuwa ƙasata. Na san uban da ya haife ni, ni ba shege ba ce, uban da ya haife ni shi ne Jimoh Audu Akpoti, don haka dole na ziyarci mahaifata”, inji Sanata.

Natasha Akpoti Mai ilimin sanin doka (Lawyer) ta sake jaddada goyon bayanta ga al’ummar mazabarta, tana kuma godiya ga soyayya da tarbar da suka yi mata duk da barazana da tsoratarwar hukumomi.

Idan za a tuna Sanata mai wakilta jihar Kogi ta tsakiya Santa Natasha ta samu kanta a halin tsaka mai wuya, tun da ta daga kara akan Shugaban Majalisar Dattijai ta kasa Sanata Godswell Akpabio, da ta zarge shi da cin zarafinta duk kuwa da kasancewar ta mai aure.

Daga bisani Majalisar Dattawa tai mata chah! tare da dakatar da ita daga zuwa da kuma wakilta yankinta a Majalisar zuwa wasu watani. Kai har ta kai anyi kutungwila na rubuta tankarda kiranye, da suna ‘yan mazabarta, domin janye ta daga wakilci.

Wanda Hukumar zabe ta kasa INEC ta fito ta sanarwa da duniya, amma INEC ta ce gaskiya ne kundin tsarin mulkin kasa shi ya bayar da hurumi na yin kiranye ga Dan Majalisar da al’ummar sa suka bukaci hakan.

Sai dai Hukumar INEC ta ce wadanda suka mika bukatar sun bar lam’a na rashin sanya lambar waya ga duk wanda ya rattaba hannunsa domin wanna bukatar da sauran wasu bayanai da suka manta basu cika ba.

Haka zalika Hukumar tsaro ta farin Kaya, ita kuma ta shiga farautar neman Sanata Natasha bisa wai ta halarci wani taro a wata kasa babu sahalewa.

Ire-iran wanna matsaloli su suke addabar Dimokaradiyar kasata Nijeriya a dake Ka, kuma a hana ka kuka.

A yau siyasar Najeriya tana fuskantar wani sabon salo na danniya, amma ya kamata a gane cewar mulki yana hannun Allah kuma al’umma ne ke da wuka da nama wajen zaɓar shugabbanin da za su jagorance su.

A Karanta Wanna:Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya kai ziyarar ta’aziya ga gwamnatin Kano da iyalan mafarauta 16 da aka halaka

A yanzu haka dai ‘yan kasa sun zuba ido domin ganin yadda wasan zai kayya ko Natasha ta cimma burin ta na kwatar hakki, ko kuma kunkuru yai mata kafa. Allah ya kyauta.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...