Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

An Yi Jana’izar Hanshakin Basarake Galadiman Kano Abbas Sunusi

Galadiman Kano
Galadiman Kano

An Yi Jana’izar Hanshakin Basarake Galadiman Kano Abbas Sunusi

Innalillahi Waina Ilahil Raji’un,
A yau Laraba 2 ga watan Afrilu,2025 Kano da Kanawa da ma Nijeriya, musamman Arewacin Nijeriya sukai rashin dattijo kuma mafi dalewa a sarauta jihar Kano, Galadima Kano Alhaji Abbas Sunusi.

An wayi gari da samun labarin rashin haziki, goggage, masanin mulki kuma Babban Dan Majalisar Sarki a gidan Dabo, Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi Bayero a rana Laraba.

Kamar yadda sanarwa ta gabata a kafofin yada labarai Galadiman Kano Abbas Sunusi ya rasu a daren Talata bayan ya sha fama da rashi lafiya kamar yadda ‘yayen sa Alhaji Abdullahi Abbas da dan uwansa, Alhaji Kabiru Abbas su ka tabbatar da rasuwar mahaifin na su bayan jinya da ya yi ta tsawon lokaci.

A Karanta Wanna:Galadiman Kano Abbas Sunusi ya Rasu

Galadiman na Kano ya kwanta dama sakamakon doguwar jiya da yai fama da ita kamar yadda muka ambata.

An haifi Abbas Sanusi a shekarar 1933 a garin Bichi, inda ya soma karatunsa a makarantar Ƙofar Kudu a shekarar 1944, sannan a shekarar 1948 ya tafi makarantar Kano Middle School da a yanzu ake kira (Rumfa College).

Tun daga wanna lokaci Alhaji Abbas Sunusi ya shiga gwagwarmayar shugabanci da jagoracin jama’a inda ya ruke mukamai da dama a masarautar Kano.

Galadima

Galadima Abbas Sunusi 

Kafin rasuwasa masanin mulki, Abbas Sunusi ya ruki mukamai daban-daban, tun daga lokacin mahaifinsa Khalifa Sarki Muhammadu Sunusi I, da Sarkin Kano Muhammadu  Inuwa da Sarkin Kano Alhaji Ado Abdullahi Bayero, wanda ya kasance a karagar masarautar daga shekarar 1963 zuwa 2014.

A Karanta Wanna:Sanata Natasha ta Dura A Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu A Kogi, Duk da Gargadin Jami’en Tsaro

Ya kasance guda daga cikin jigogin da suka shahara a masarautar Kano haka kuma Galadima yayi ficce wajen iya ado a tsakanin Hakiman Kano. A zamanin marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, shi ne Wamban Kano, Kuma Babban Dan majalisar Sarki.

Kafin rasuwasa Abbas Sunusi Yana daga cikin mafi dalewa a sarautar jihar Kano mai daraja da kuma tarihi.
Tun a Karon farko mahaifinsa Sarki Khalifa Muhammadu Sunusi na I, ya naɗa masa rawanin Sarkin Dawakin Tsakar Gida kuma Hakimin Ungogo a shekarar 1959.

A shekarar 1963 kuma ya zama Ɗan Iyan Kano a zamanin mulkin Sarki Muhammadu Inuwa, sannan likafa tai gaba inda aka mai da shi Wamban Kano kuma Babban dan Majalisar Sarki a lokacin Sarki Kano Alhaji Ado Abdullahi Bayero.

Haka kuma a lokacin mulkin Sarki Muhammadu Sunusi II, na farko ne aka sake ɗaga  likafar sa zuwa matsayin Galadiman Kano har lokacin da Allah ya karbi ransa.

Alhaji Abbas Sunusi kawu ne ga Sarki Muhammadu Sunusi II, kuma mahaifi ga shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas.

A Karanta Wanna:Gwamnatin Kano ta karrama Hazikan Gasar karatun Alkur’ani

Galadiman Kano ya rasu yana da shekaru 92 kuma shi ne dattijo mafi tsufa a duk Masarautar Kano. Ya rasu ya bar mata da ‘yaya 35, daga cikinsu akwai shugaban jami’iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas.

Daruruwan mutane ne suka halarci Jana’izar Galadiman Kano daga ciki da wajen jiha. Limamin Kano Farafesa Nasiru Zaharardeen shi ya jagoranci Sallar Jana’izar. Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf da ‘yan Majalisar zartarwa ta kano da tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso da ‘yan Majalisar Dokoki ta jiha da Sarkin Sunusi na II, da Hakimai da masu mulki daban-dabam da ‘yan siyasa da attajirai da sauran daukacin jama’a na daga cikin wadanda suka halarci Sallar Jana’izar.

An kuma gudanar da jana’izarsa a fadar masarautar Kano, dake kofar kudu da karfe 10 na safiyar ranar larabar a inda aka bine gawarsa a makabartar Gandun Albasa.

A Karanta Wanna:Sarkin Musilmai Abubakar Sa’ad Ya tabbatar da ganin watan Shawwal

Muna rokon Allah Subahanahu Wata’ala da ya gafartawa Galadima Alhaji Abbas Sunusi kurakuran sa ya kuma shigar da shi Aljanar Firdausi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...