Kabilu Mazauna Malam Madori da Ƙaugama Sun Karrama Ɗan Majalisa Tarayya Hon. Makki Yalleman Bisa Kulawa Ga Ilimi
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: Mazauna Kusa Da Madatsar Ruwa ta Ghari Da Su Yi Nesa Da Kogi – Inji Shugaban Ƙaramar Hukuma
Ƙabilun Ibo da Yarabawa da Igala gami da Ibibio mazauna Ƙaramar Hukumar Malam Madori da Kaugama sun Karrama Ɗan Majalisar Tarayya Hon. Makki Abubakar Yalleman bisa amfanuwa da wakilcinsa ba tare da nuna bambanci ba gami da bada tallafin ilimi ga ‘yayen su.
Shugabannin ƙabilun sun ce salon mulkinsa abin a yaba ne, duba da yadda yake samar da shirye-shirye masu ma’ana waɗanda ke bunkasa ci gaban al’umma.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
EFCC ta Gurfanar Da Ɗan Austria Kan Boye Bayyana Wasu Maƙudan Kuɗaɗe $800,575 da €651,505
Shugaban kungiyar mazauna Malam Madori da Kaugama (Non-indigene Association ) Mr. Celestine, shi ya bayyana haka a lokacin da suka kai masa ziyara girmamawa tare da bashi shedar karramawa a gidansa a ranar Asabar da ta gabata.
Shugaban ya ce shirin bada Tallafin Ilmi mai taken (Educational Support) wanda yake ƙarƙashin kulawar Maiunguwa, Ibrahim Zakar Al-kampaly da gabatar da ƙudiri a Majalisa gami da samar da muhimman ayyukan more rayuwa da taimakon al’ummar sa musamman na mazabar Malam Madori da Kaugama abin sam barka ne.
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Majalisar Dokokin Kano ta goyi bayan Gwamna Yusuf Ya fita Daga Jam’iyyar NNPP
Shugaban ya ce duba da irin wannan ayyukan alkhairi suka ga dacewar su ƙarrama shi, sun kuma roƙe shi da ya ci gaba da irin waɗannan ayyuka kamar yadda ya saba.




























