Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

UNICEF Ta Ce Yaro Ɗaya Na Mutuwa Daga Cikin 10 Sakamakon Rashin Tsaftattacen Makewayi

UNICEF
UNICEF

Daga Wakilinmu

Binciken UNICEF ya nuna cewa a ƙalla yaro ɗaya kan rasu a kullum sanadiyar rashin tsaftattacen makewayi a Africa.

Wakiliyar Asusun Tallafawa ƙananan yara na Majalisar ɗinkin duniya, (UNICEF) a ƙaramar hukumar Nassarawa, Hajiya Fatima Yusuf Falgore, ita ta sanar da hakan a wata ganawa ta musamman wacce ta ƙunshi wakilan ƙaramar hukumar da sarakuna al’umma na yankin, don faɗakar da su alfanun tsaftattacen makewayi, wanda aka gudanar a shalkwatar ƙaramar hukumar ta Nassarawa a ranar Talata.

Ka karanta wanna: Ko Ka San Burushin Wanke Haƙora Na Iya Tasiri Ga Lafiyar Baki Da Jikin Dan Adam?

Fatima Falgore, ta ce ƙididdigar baya-bayan nan da kwararu suka gudanar ita ta tabbatar da hakan wadda Najeriya tana daga cikin ƙasashen, inda ta ce wannan gagarumar matsala ce da ya kamata al’umma su farga akanta wajen ɗaukar matakan kawar da ita a kan lokaci tun kafin taci karfinsu, musamman ta labi’antuwa da tsaftar makewayi a ko da yaushi.

Ka karanta wanna:Ƴar Tik Tok Ta Yi Ɓatan Dabo: Al’ummar Kano Na Ce-Ce-Kuce Kan Sharuɗɗan Beli

Wakiliyar UNICEF, ta ce,” Na yi imani irin wanna ganawa da wakilan jama’a kan muhimmancin kula da makewayi zai taimaka ƙwarai da gaske domin daƙile yaɗuwar cututtuka masu saurin hallaka yara ƙanana da mata masu juna biyu sakamakon gurbacewar Mahalli.”

A jawabinsa , mai rukon muƙamin shugabancin ƙaramar hukumar Nassarawa, Alhaji Auwalu Makama Dambatta, ya shawarci Sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa-da-tsaki a yankin da su baiwa shirin gwamnati na kare lafiya da tsaftar muhalli da samar da kyakyawan ruwan sha cikakkiyar kulawar da ta dace don magance yaɗuwar cututtuka da gurbacewar muhalli.

Ka karanta wanna:Kasuwancin Awara Ya Bunƙasa a Sanadiyyar Ɓarkewar Yunwa a Kano
Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar Nassarawa, Malam Usman Muhammad Kabir, ya ce Shugaban Ƙaramar Hukumar, ya kuma yabawa jami’en UNICEF, a ƙoƙarinsu na faɗakar da jama’a, gami da jaddada ƙudirin gwamnati mai ci na farfaɗo da shirin shiga-gida domin faɗakar da su muhimmancin tsaftar mahalli da kula da makewayi.

Danbatta ya ce, a kwai shiri na musamman da ƙaramar hukumar za ta bujiro da su waɗanda su ka jiɓanci dabarun inganta harkar lafiya da samawa al’umma tsaftataccen ruwan sha da makewayi a makarantun gwamnati dana tsangaya da kasuwanni da tashoshin mota da sauran wuraren haɗuwar jama’a domin hana tsuguno barkatai.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...