Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

LALATA:YAN SANDA NA TUHUMAR MAHAIFI DA YI WA YARSA CIKI A JIHAR BAUCHI

CP Bauchi Sani Aliyu
CP Bauchi Sani Aliyu

LALATA:YAN SANDA NA TUHUMAR MAHAIFI DA YI WA YARSA CIKI A JIHAR BAUCHI

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Rundunar Yan sanda ta jihar Bauchi na ci gaba da bincike kan Wani magidanci da ake zargi yana azabtar da ‘yar cikin sa a lokacin da ya bukaci yin fasadi da ita, yadda daga bisani ta Kai ga samun juna biyu.

A ranar Alhamis, 3 ga Afrilu, 2025 da misalin karfe 4:30 na yamma, rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta karɓi ƙorafi daga wani mai suna Abdullahi Baban Karatu, mai shekaru 55 daga kauyen Kurmin Ado, a gundumar Kariya Ward, a karamar hukumar Ganjuwa, jihar Bauchi.

Abdullahi ya kai korafi wani mutumi mai suna Umar Alhaji Sule, ɗan shekara 50, mazaunin kauyen Kurmin Ado, bisa zarginsa da yin da lalata da ‘yarsa, mai shekara 17, wace har tasamu juna biyu.

A Iya Karanta Wanna:Iftula’i: Mata biyu sun haɗu da ajalisnsu sakamakon Faɗawa Kudiddifi A Kano

Rundunar ta tura ƙwararrun jami’ai don gudanar da binciken sirri tare da kama wanda ake zargin.

A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa laifinsa, yana mai cewa ya sha kwantawa da yar tasa, hakan ya kai ga ta daukar ciki na wata uku kamar yadda rahoton likita ya tabbatar.

A lokacin da aka yi wa yarinyar tambaya, ta tabbatar da abin da mahaifinta ya fada, inda ta bayyana cewa lamarin ya faru ne lokacin da mahaifiyarta ta tafi garin iyayenta a Burra, karamar hukumar Ningi, kuma mahaifinta ya yi amfani da damar don aikata laifin. Bayan dawowar mahaifiyar, ta lura da sauyin yanayin jikinta wanda ya nuna tana da juna biyu. Kuma ta bayyana ta ce mahaifinta ne ke da alhakin yi mata cikin ta hanyar tursasa mata da kuma yi mata barazana da duka don kada ta tona masa asiri.

A Iya Karanta Wanna:Asiri Ya Tonu: Saura Kiris Wayar Salula ta Haɗa Auren da Babu Wali Ba Siga

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, psc(+), mni, ya bayar da umarnin a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala binciken.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...