Iftula’i: Mata biyu sun haɗu da ajalisnsu sakamakon Faɗawa Kudiddifi A Kano
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano dake Arewacin Najeriya, ta tabbatar da mutuwar wasu mata su biyu sakamakon faɗawa wani kudiddifi a garin Gezawa dake jihar Kano.
Read also: Mutane 16 Gini Ya Faɗawa A Unguwar Dandishe A Kano
Kakakin Hukumar na jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa a daren jiya Talata, inda ya ce lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar.
A Karanta Wanna:Gwamnatin Tarayya Haɗin Gwiwa da Bauchi Sun Samar da Motocin Daukar Marasa Lafiya Kyauta
A cewar Saminu, “Da misalin karfe 11:15 na safiyar jiya Talata ne muka sami kiran neman agajin gaggawa, ta hannun shugaban jami’an sintiri na ƙaramar hukumar Gezawa, sakamakon faruwar wani iftula’i, a inda ya sanar da mu fadawar Matan biyu cikin Kudiddifi inda ake ta neman su tun daren ranar Litinin ɗin da ta gabata, lamarin da ya sanya muka tura jami’an mu domin ceto su”.
Bayan sun je sun sami nasarar ciro Matan inda aka tabbatar da cewa sun rasu, mafari kenan da suka damka su a hannun jami’in ɗan sandan dake aiki a ofishin ‘yan Sanda na ƙaramar hukumar Gezawa wato Musa Garba”.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
A Karanta Wanna:Asiri Ya Tonu: Saura Kiris Wayar Salula ta Haɗa Auren da Babu Wali Ba Siga
A ƙarshe sanarwar hukumar ta ce musabbabin faruwar Iftila’in shine a sakamakon zuwa da suka yi domin su ɗauraye jikinsu, bayan sun taso daga wurin aikin sarrafa zoɓo da suke yi a wani kamfani da ke yankin.




























