Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

AN YI KARE JINI BIRI JINI DA YAN BINDIGAR DA SUKA TARWATSA WASU YANKUNAN ALKALERI A BAUCHI

Alkaleri Bauchi
Alkaleri Bauchi

AN YI KARE JINI BIRI JINI DA YAN BINDIGAR DA SUKA TARWATSA WASU YANKUNAN ALKALERI A BAUCHI

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Ruhotanni da ke fitowa daga karamar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi Yan bindiga masu garkuwa da mutane (kidnappers) sun saka al’ummar wasu yankunan karamar hukumar Alkaleri a gaba, yadda mutane da dama ke gudu daga yankin Gwana da Kafin Duguri da Kargo da Gobirawa da Futuk da Pali da wasu yankunan da dama.

Malam Sani Maihajja Futuk ya bayyana mana tun ranar Lahdi Yan bindiga suka tarwatsa garin hakimin Gwana, suka kashe Soja biyu da Dan banga daya.
Yayin da suma mutanen gari da Yan banga da jami’an tsaro suka yi kukan kura suka kashe mutanen Yan bindigar da dama.

Bayan haka Yan bindigar sun kama mutane da dama sun shiga daji da su kuma sun Kona gidaje da dukiya mai yawa.

Ya zuwa wannan lokacin mutanen yankin Mansur da Digare da Duguri suna Kwarara zuwa garin Futuk a cikin motoci da tabare da sauran abubuwan hawa.

Ɗan Jarida Zai Gurfanar da Hadimin Gwamna Kano a Kotu, Sakamakon Zargin Cin Zarafi

A safiyar wannan talata Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na jihar Bauchi ya kwashi Yan jarida da jami’an tsaro shima ya tafi yankin don gani da ido tare da jajantawa.

Yan bindigar an bayyana cewa an jima ana ganin su a dazukan yankin da gandun dajin Yankari har zuwa wannan lokacin da aka gansu cikin motocin akori kura suna harbin kan mai uwa da wabi lamarin da ya salwantar da rayuka da dama ya kuma raunata mutane da dama ya raba wasu da gidajen su.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da cewa ‘yan bindiga sun kai hari a yankin kasar Gwana da ke karamar hukumar Alkaleri. Haka kuma Yan bindigar sun kai wa al’ummar garuruwan hari da kuma sansanin rundunar haɗin gwiwa ta JTF a ranar 22 ga watan Fabrairu na shekarar 2026, da misalin ƙarfe 4:32 na yamma.

A cewar SP Nafiu Habib, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, harin ya janyo asarar rayuka inda sojoji biyu daga rundunar 33 Artillery da ke Bauchi da wani ɗan sa-kai suka rasa rayukansu yayin musayar wuta da ’yan bindigar.

Rahoton ya ƙara da cewa mutane uku daga cikin al’ummar yankin an yi garkuwa da su, yayin da rundunar yaki da garkuwa da mutane ta ’yan sanda ta yi nasarar hallaka ’yan bindiga bakwai a lokacin artabun.

Rundunar ta bayyana cewa an tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya da kare fararen hula da suka rasa matsugunan su, tare da hana aukuwar wasu hare-haren nan gaba.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya tabbatar wa jama’a cewa ana ci gaba da sa ido da tattara bayanan sirri domin gano inda ’yan bindigar da suka tsere suke tare da kama su, da kuma ceto mutanen da aka sace.

Aƙalla Ɗalibai Mata Dubu 12,133 Zasu Sami Tallafin Karatu Na AGILE A Bauchi

Rundunar ’yan sanda ta ce za ta rika fitar da ƙarin bayani yayin da al’amura ke ci gaba da bayyana don sanar da kowa halin da ake ciki game da tsaro a jihar Bauchi.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Rahoto Kwararu Ya Ce Hare-Haren Garkuwa Da Mutane Ya Ƙaru da Kaso 66% Akan Shekarar 2025 A Najeriya - The StentorNews Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...