Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

HISBAH A BAUCHI TA HUKUNTA MATASAN DA SUKA DAURA AUREN SADAKIN N3000

Amarya da Ango Bauchi
Amarya da Ango Bauchi

HISBAH A BAUCHI TA HUKUNTA MATASAN DA SUKA DAURA AUREN SADAKIN N3000

Daga Muazu Hardawa Bauchi

Hukumar Hisbah a jihar Bauchi ta hukunta matasa bakwai da ake tuhuma da gudanar da aure ba bisa kaida ba kan sadakin naira dubu Uku a garin Bauchi.

Idan za a tuna Jaridar TSN Hausa a makon jiya ta kawo muku labarin wasu matasa a unguwar mahaukata da ke Bauchi suka shirya gudanar da auren tsakanin Kamila Shehu da Mohammed Chindo kan sadakin naira dubu uku duk da cewa babu sani ko amincewar iyaye sun gudanar da auren kafin daga baya aka tattara amaryar da angon da masu shaida a yayin farmaki cikin dare a gidajen iyayen su.

Yan kungiyar sintiri ta Umar Shayi vigilante sune suka dafe Yaran a gidajen su a unguwar mahaukata daga bisani suka kai su ofishin Yan sanda na Township suka ajiye su na kwanaki.

An Nemi a Gyara Auran Matasa Da Sukai Aure Akan Sadaki ₦3000, A Maimakon Dauri

Daga karshe kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi Nafiu Habib ya bayyana cewa sun rike matasan sun gudanar da bincike kafin suka hannata su a hannun hukumar Hisbah don fiskantar hukunci. Yace laifin su ba mummunan laifin da za a hana belin su bane. Kuma a cikin su akwai yaron da ke karatu a Federal Polytechnic yana da jarrabawa shi aka fara saki a matsayin beli ya tafi jarrabawa.

Kwamiahinan Hisbah Bar Aminu Balarabe Isah ya bayyana cewa sun hukunta Yaran ta hanyar bulala da aikin kwashe Shara a unguwannin su, na tsawon mako biyu. Yace Yaran sun yi laifin daura auren ba tare da amincewar iyaye ba kuma ba tare da karban sadaki da Shariar musulunci ta amince ba.

Don haka Bar Aminu Balarabe ya gargadi iyaye su rika auras da Yaran su idan sun kai lokacin aure sun bukaci auren. Ya ce saboda Yaran suna da abin yi amma an jinkirta musu auren don haka suka yi gamon kan su tare da kulla auren bisa son rai.

Hukumar Kamfanin Fortune Rice Ta Musanta Labarin Rufe Kamfanin Bisa Zargin Karya Dokar Muhalli

Uwargidan gwamnan jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Mohammed ta bukaci iyaye su rika sauke nauyin da Allah ya dora musu ta hanyar sanya ido kan tarbiyyar Yara maza da mata manya da kanana don su taso mutanen kirki da za a yi alfahari da su.
Don haka ta sanya ido kan wannan lamarin tun daga farkon sa har karshe tare da ganin ba a kai su kotu don musu cajin da zai kai su gidan yari sake dauko mummunan hali ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...