Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Hukumar Kamfanin Fortune Rice Ta Musanta Labarin Rufe Kamfanin Bisa Zargin Karya Dokar Muhalli

Fortune rice mills ltd
Fortune rice mills ltd

Hukumar Fortune Rice Ta Musanta Labarin Rufe Kamfanin Bisa Zargin Karya Dokar Muhalli

Daga Sunusi K/Naisa

Hankalinmu ya kai kan wasu rahotanni da ke yawo a wasu kafafen yada labarai dangane da rufe kamfanin sarrafa shinkafar mu na fortune Rice mills dake rukunun masana’antu na Sharada da Hukumar Kula da Ka’idojin Muhalli ta Kasa (NESREA) ta yi bisa zargin karya dokokin muhalli.

Duk da cewa mun amince da alhakin da NESREA ke da shi na tabbatar da bin ka’idojin muhalli, muna ganin ya dace mu fayyace wasu batutuwa domin a samu daidaitaccen bayani tare da kwantar wa jama’a, abokan hulɗarmu da kuma al’ummar da ke zaune a yankin hankali.

Fortune Rice

Da farko, kamfanin mu na fortune Rice ya kasance yana gudanar da ayyukansa bisa tsarin dokokin Najeriya tare da ci gaba da jajircewa wajen kiyaye ingantattun ka’idojin muhalli da masana’antu. A matsayinsa na kamfani mai kishin al’umma, mun bayar da gudunmawa sosai tsawon shekaru wajen bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma inganta wadatar abinci a Jihar Kano da ma kasa baki ɗaya.

Tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman Ya Faɗa Komar EFCC

Mun lura da koke-koken da aka gabatar dangane da ƙurar da ake zargin tana fita daga kamfanin, hakan baya nufin mun yi shakulatn bangaro da hanyoyin kiyaye wada lafiyar mazauna kusa da kamfanin ba, Sai dai yana da muhimmanci a bayyana cewa tuni kamfanin ya dauki matakai na gyara da inganta ayyukansa domin ƙara ingancin aiki tare da ƙarfafa tsarin kula da muhalli a cikin harabar masana’antar.

Saɓanin yadda Hukumar NESREA ke ƙoƙarin nuna lamarin, mahukuntan kamfanin ba su yi biris da tattaunawa da hukumomin ba, Mun ci gaba da kasancewa cikin hulɗa da hukumomin da abin ya shafa tare da nuna cikakken shirin ba da haɗin kai wajen magance duk wasu matsalolin da aka gano yayin bincike.

Haka kuma muna son tabbatar wa mazauna yankunan da ke kewaye da kamfanin cewa lafiyarsu, tsaronsu da walwalarsu na da matuƙar muhimmanci a gare mu. Kamfanin bai taɓa yin wani abu da gangan da zai iya jefa lafiyar jama’a cikin haɗari ko lalata muhalli ba.

A cikin fahimtar juna da haɗin kai, a halin yanzu muna aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙwararrun masana muhalli da hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da cewa an warware duk sauran matsalolin bisa tanadin dokokin muhalli na ƙasa.

An Nemi a Gyara Auran Matasa Da Sukai Aure Akan Sadaki ₦3000, A Maimakon Dauri

Saboda haka muna kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da guje wa yaɗa bayanan da ba su da sahihanci waɗanda za su iya haifar da rashin fahimta ko kuma bata sunan kamfani da ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arzikin yankin.

Kamfaninmu na fortune Rice zai ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukan masana’antu cikin nagarta, kare muhalli da kuma zaman lafiya da al’ummomin da ke kewaye da shi.

sanarwar da Manajan Daraktan kamfanin
Alhaji Shehu Dalhatu Shehu yasanyawa hannu:

Amadadin Shugaban kamfanin sarrafa Shinkafa na fortune Rice
Alhaji Dalhatu Shehu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...