Tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman Ya Faɗa Komar EFCC
Daga Adita
Jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta Economic and Financial Crimes Commission sun cafke tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman bayan ya shafe lokaci yana ɓuya duk da hukuncin da aka yanke masa.
Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar hukumar.
EFCC ta Gurfanar Da Ɗan Austria Kan Boye Bayyana Wasu Maƙudan Kuɗaɗe $800,575 da €651,505
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Ya ce an kama Mamman ne da misalin karfe 3:30 na daren Talata a yankin Rigasa da ke jihar Kaduna.
EFCC BATA KAI MANA MAMAYA BA – DANGOTE
Read also: An Caka wa Malamin Addini Wuka a Sakkwato, Masu Ibada Sun Kashe Wanda Ake Zargi
Mamman dai na cikin waɗanda aka yankewa hukuncin ɗaurin shekaru 75 a gidan yari, sai dai ya ɓuya bayan yanke hukuncin.
Hukumar EFCC ta ce za ta ci gaba da ɗaukar matakan doka a kansa.




























