Gwamna Kano Abba Ya Amince da Rushe Hukumar Kula da Kare Haƙƙin Maissye da Matsayar wa ta Kano Nan Take
Daga Edita
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da rushe hukumar kare haƙƙin masu amfani da kaya ta Jihar Kano nan take sakamakon rashin fahimta tsakanin jagororin hukumar.
An bada sanarwar haka ta hannun mai magana da ofishin Sakataren Gwamnatin jihar, Musa Tanko Muhammad. Sanarwar ta ce rikicin shugabanci da ya dade yana addabar hukumar, na daga cikin ummul-aba’isin rushe hukumar duk da ƙoƙarin gwamnati na sasanta bangarorin da ke rikicin, amma hakan ya ci tura.
Read also: Ɗan Jarida Zai Gurfanar da Hadimin Gwamna Kano a Kotu, Sakamakon Zargin Cin Zarafi
Ga Wani Labarin:“Na Fasa Auren Yar Guda”, In ji Mai Wushirya
Sanarwar ta tabbatar da korar shugaban hukumar da Sakataren Zartarwa, da kuma dukkan mambobin hukumar, har da mambobin da ke matsayin wakilai (Ex-Officio), daga mukamansu daga yau Asabar, 25/10/2025.
Yayin da yake isar da wannan umarni daga Gwamna, Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ya umarci dukkan waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar ofisoshinsu tare da dukkan kayan gwamnati da ke hannunsu ga mafi girman jami’in hukumar kafin ƙarshen lokacin aiki na ranar Litinin, 27 ga Oktoba, 2025.
Read also: Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano
Ga Wani Labarin:Magidanci Mai Mata 2 Ya Kashe Ɗan Achaɓa Don Samun Kuɗin Ƙarin Aure
Sakataren Gwamnatin, ya kuma bayyana cewa dukkan takardun miƙa ragamar aiki su kasance an miƙa su zuwa Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Sashen Bincike da Kimantawa da Harkokin Siyasa (REFA),da kuma ofishin Mai Girma Kwamishina na Ma’aikatar Zuba Jari da Kasuwanci.




























