Kotu ta Umarci Masu Barkwanci Na TikTok A Kano Dasu Yi Aure Bayan Yaɗa Bidiyon “Futsara”
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: Kotu a Kano ta Daure ‘yan tiktok Shekara Guda Bisa Laifin Wallafa Bidiyon Batsa
Kotun Majistare a Kano ta umarci shahararrun masu TikTok biyu, Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda, da su yi aure cikin kwanaki 60 bayan da aka same su da laifin wallafa bidiyoyi na rashin kunya a kafafen sada zumunta.
Wannan hukunci ya biyo bayan ƙarar da aka shigar a kansu bayan da bidiyon da suka wallafa suka yadu a intanet, inda aka yi la’akari da su a matsayin masu keta ɗabi’a da sabawa ƙa’idojin addini da al’adu da ake mutuntawa a jihar Kano.
A cewar Hukumar Tace Fina-finai da Bidiyo ta Jihar Kano, bidiyon sun nuna yadda ma’auratan ke nuna soyayya da akaita futsara wanda bai kamata jama’a su kalla.
Ga Wani Labarin:Magidanci Mai Mata 2 Ya Kashe Ɗan Achaɓa Don Samun Kuɗin Ƙarin Aure
Read also: Zargin Almundahana: Kotu Ta Umarci Bankin UBA Ya Riƙe Kuɗin Kano Da Aka Karkatar
Hukuncin ya tayar da ce-ce-ku-ce sosai a dandalin sada zumunta, inda wasu ke tambayar ikon kotu na tilasta aure a matsayin hukunci, yayin da wasu kuma suka goyi bayan matakin, suna kiran sa a matsayin hanya ta kare ɗabi’a da mutuncin jama’a.
Majistare Halima Wali ta umarci hukumar Hisbah ta Jihar Kano da ta taimaka wajen shirya auren.
Ta gargade su cewa, rashin yin auren cikin lokacin da aka kayyade zai zama rashin girmama kotu.
Kotu ta kuma umarci shugaban Hukumar Tace Fina-finai da Bidiyo ta Jihar Kano da ya kula da yadda za a aiwatar da wannan umarni na aure.
Masu TikTok ɗin biyun an gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin samarwa da yaɗa bidiyo masu zubar da mutunci a kafafen sada zumunta.
Mai Wushirya an tura shi gidan gyaran hali bayan bidiyon da ke nuna shi yana yin abin da hukuma ta bayyana a matsayin “aikata halayen iskanci da wulakanci” tare da wadda suka yi bidiyon ta yadu.
Read also: Kotu Ta Daure Wani Mutum Wata 3 A Gidan Gyaran Hali Sakamakon Kona Taya A Kano
Ga Wani Labarin:Yan Sanda Sun Kama Wand Ya ƙwaƙule Idon Kanwar Sa Da Kuma Bokan Da Ya bashi Sa’ar
Hukumar Tace Fina-finai ta bayyana cewa bidiyon sun karya dokokin jihar da ke haramta samarwa da yaɗa balala da abubuwan da ke da saƙon batsa ko motsin sha’awa.



























