Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

DA ƊUMI-ƊUMI: Wasu Fusatattun matasa sun kashe DPO ‘Yan Sanda har lahira a Kano

Rano Police Division
Rano Police Division

Wasu Fusatattun matasa sun kashe DPO ‘Yan Sanda har lahira a Kano

Wasu Fusatattun matasa a Karamar hukumar Rano sun fara wa Baturen ‘yan Sanda na yankin har ofishinsa, wanda hakan yai sanadin rasuwarsa.

Majiyarmu ta ce matasan sun aikata wannan danyan aiki ne bayan da suka sami bayanin DPO ya yiwa abokin su duka wanda har ya ta kai ga sanadin rasuwarsa.

Samun labarin ke da wuya matasan sukai gungu inda suka iske jami’en tsaron har ofis, kuma ana mai faruwa ta faru.

A Iya Karanta Wanna:Dokar hana bayyana tsiraici: Ibrahim Traore ya sanya biyan tarar Miliyan 2 da ɗauri na dindindin ga wacce aka kama

Majiyar ta ce fusatattun matasa sun farwa Ofishin ‘yan sandan bisa zargin ya kashe wani ɗan uwansu,  da  ake zargin ya karya doka ta  gudanar da wani gangamin rally a babura.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da rasuwar DPO na Ƙaramar hukumar Rano a wata sanarwar da Kakakin rundunar ‘yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa ya a daren Litinin.

Ya ce tuni an kama mutane 27 da ake zargi da hannu a cikin lamarin, tare da tabbatar da dawo da zaman lafiya a yankin na Rano.

A Iya Karanta Wanna:‘Yan sanda a Kano Sun Chafke Likitan Bogi da Wani Matashi Bisa Zargin Zubar da Ciki Da Aikata Kisan Kai

Abdullahi Kiyawa ya ce Kwamishina ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori ya bada tabbacin rundunar zata gudanar da bincike tare da gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kuliya.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...