Zamu Rinƙa Ciyar da Ma’aikatan KAROTA Gaba A Kan Lokaci, In Ji MD Faisal Mahmoud
Daga Sunusi K /Naisa
Read also: ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Asibitin Kaduna Tare da Sace Ma’aikatan Jinya
Manajan Darakta na Hukumar Kula da Zirga-Zirga Ababan Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), Faisal Mahmud Kabir, ya tabbatar wa ma’aikatan hukumar na ƙara musu girma akai-akai domin ƙarfafa musu gwiwa wajen aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata.
Hon. Faisal Mahmud Kabir ya bayar da wannan tabbaci ne yayin da yake jawabi ga shugabannin sashen zirga-zirga 918 da ke cikin birnin Kano.
Read also: Shugaban Hukumar KAROTA Ya Karɓi Baƙuncin Shugabannin Hukumar Kashe Gobara Ta Tarayya, Reshen Kano.
Manajan Daraktan, wanda Daraktan Harkokin Gudanarwa da Mulki na Hukumar, Alh. Mahmud Haido, ya wakilta, ya tabbatar wa ma’aikatan cewa daga yanzu duk wani ma’aikaci da aka ƙara masa girma zai ci moriyar hakan a albashinsa.
Sai dai kuma, ya gargaɗi ma’aikatan da su guji ƙin zuwa wurin aiki, yana mai cewa duk wanda aka samu yana ƙin zuwa aiki za a ɗauki mataki mai tsanani a kansa bisa tanadin dokokin aikin gwamnati na Jihar Kano.
Read also: Hukumar KAROTA Ta Fara Sanya Ido da Sintiri Kan Masu Aiki da Achaba (Okada) a Birnin Kano
Hukumar KAROTA Ta Fara Sanya Ido da Sintiri Kan Masu Aiki da Achaba (Okada) a Birnin Kano
Ma’aikatan na kukan cewa da sau da yawa ƙarin girma a hukumar KAROTA yana kasancewa ne kawai a rubuce ba tare da an sayawa ma’aikacin a albashi ba wato (notional).



























