Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Hukumar KAROTA Ta Fara Sanya Ido da Sintiri Kan Masu Aiki da Achaba (Okada) a Birnin Kano

Achaba
Achaba

Hukumar KAROTA Ta Fara Sanya Ido da Sintiri Kan Masu Aiki da Achaba (Okada) a Birnin Kano

Daga Sunusi K/Naisa

Biyo bayan haramta aikin ‘yan achaba da Gwamnatin Jihar Kano ta yi, Hukumar Kula da Hanyoyin Mota ta Jihar Kano (KAROTA) tare kwamatin Karta Kwana na Jamia’an Tsaro sun fara sintiri da sanya idanu a wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano daga ranar Larabar nan, domin gano masu karya dokar.

Kamar yadda aka sani, Gwamnatin Jihar Kano ta hanyar Ma’aikatar Yada Labarai ta sanar da dakatar da aikin achaba a kwanan nan domin rage matsalar rashin tsaro da ke karuwa a wasu sassan jihar, da ake zargin yana da nasaba da dawo da aikin Achaba a cikin birnin Kano.

A yayin da ya ke bayyana hakan, Manajan Darakta na KAROTA, *Hon. Faisal Mahmud Kabir* ya ce jami’an hukumar tare da sauran Jamia’an Tsaro za su kai mamaya zuwa wuraren da aka samu rahoton dawowar ‘yan achaba domin tabbatar da bin umarnin gwamnati.

Ma’aikatar Ilimi ta Kano Ta Ayyana Ranar Hutu Na Zangon Karatu Na Farko

Don haka Hon. Faisal Mahmud Kabir ya gargadi masu achaba da su daina wannan aiki daga yanzu, in ba haka ba su fuskanci fushin Hukuma.

Ya kuma bukaci jami’an KAROTA da su shirya tsaf domin aiwatar da wannan doka yadda ya kamata.

Rundunar Ƴan sanda ta Hana Goyo a Babur a Kano

Manajan Daraktan ya jaddada cewa Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, *Alhaji Abba Kabir Yusuf* na da matukar damuwa da duk wani abu da zai iya barazana ga rayuka da dukiyoyin jama’a.

Sa hannu:
Abubakar Ibrahim Sharada Anipr
Jami’in hulda da jama’a na hukumar (Karota) Kano State.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...