Shugaban Hukumar KAROTA Ya Karɓi Baƙuncin Shugabannin Hukumar Kashe Gobara Ta Tarayya, Reshen Kano.
Daga Abubakar Sharada
Read also: Hukumar KAROTA Ta Fara Sanya Ido da Sintiri Kan Masu Aiki da Achaba (Okada) a Birnin Kano
Shugaban Hukumar KAROTA Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya karɓi baƙuncin shugabannin Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya ƙarƙashin jagorancin DSF Suleiman S. Adam, a wata ziyara ta musamman da suka kai ofishin KAROTA, a birnin Kano.
Ziyarar na daga cikin bikin shekara-shekara da Hukumar Kashe Gobarar ke gudanarwa, wanda ke da nufin ƙarfafa haɗin kai da musayar kwarewa tsakanin hukumomin gwamnati da na tsaro a fadin jihar.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Yayin karɓar baƙuncin tawagar, Shugaban KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya nuna jin daɗinsa da godiya bisa wannan ziyara, tare da yabawa hukumar kashe gobara bisa rawar da take takawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar Kano.
Shugaban ya bayyana cewa KAROTA za ta samar da wani sashe na musamman da zai ba da gudunmawa wajen ayyukan ceto da taimakon gaggawa, musamman idan gobara ko haɗurra suka auku a cikin birnin Kano.
Read also: DA DUMI-DUMI; Jami’an Hukumar DSS Ta Kama Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo
A nasa jawabin, DSF Suleiman S. Adam, ya jaddada bukatar ƙara haɗin kai tsakanin hukumomin biyu, domin tabbatar da tsaro, tsabtace muhalli, da ingantaccen tsarin ceto a jihar.
A ƙarshe, Shugaban KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya jaddada cewa irin wannan haɗin kai shi ne ginshiƙin ci gaba, inda ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da yin aiki tare da dukkan hukumomin tsaro da ceto a jihar Kano domin inganta rayuwar jama’a da kare muhalli.



























