Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

DA DUMI-DUMI; Jami’an Hukumar DSS Ta Kama Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Bello Bodejo

Bello
Bello

Rahotonni sun tabbatar jami’an tsaro na farin kaya wato DSS su chafke Shugaban ƙungiyar Khautul Hore, Kan kafa rundunar sa-kai ta Fulani a Jihar Nasarawa.

Wasu daga cikin shuagabannin kungiyar ta Kautal Hore kuma makusanta ga Bello Bodejo sun tabbatar wa da kafar yaɗa labarai ta BBC batun kama Bodejo a yau Talata.

Sun ce jami’an DSS tare da wasu sojojin Najeriya suka kama shi a garin Lafiya babban birnin jihar Nasarawa.

Sai dai sun ce suna bin bahasi domin ba su san inda aka tafi da shi ba.

A ranar Laraba 17 ga watan Janairu Bello Badejo ya ƙaddamar da rundunar a garin Lafiya inda ya ce za ta taimaka wajen yaƙar ɓarayi da ɓata-gari daga cikin Fulani

Bayanai na cewa jami’an tsaron Najeriya sun kama Bodejo ne kan fargabar cewa kirkiro da ƙungiyar sa-kai zai iya janyo tashin hankali a faɗin ƙasar, kuma kasancewar ba ta da rijista da hukumar farin kaya ta DSS.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...